Zaben 2027: Jam'iyyar NDC Ta Su Kwankwaso da Obi Ta Samu Babbar Nasara a Kotu
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci INEC ta amince da sabon tambarin Nigeria Democratic Congress (NDC) domin amfani da shi a zaɓe
- Kotun ta hana INEC dakatarwa ko tsoma baki wajen amfani da alamar nasara ta yatsu biyu da NDC ta ƙirƙira a matsayin tambarinta
- Hukuncin ya biyo bayan ƙarar NDC, bayan da jam’iyyar ta zargi INEC da cire sabon tambarinta tare da mayar da tsohon tambari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta amince tare da amfani da sabon tambarin jam’iyyar NDC a duk zaɓukan da za ta gudanar.
Kotun ta kuma hana INEC dakatarwa ko tsoma baki wajen amfani da alamar nasara mai yatsu biyu da jam’iyyar ta ƙirƙira a matsayin tambarinta.

Kara karanta wannan
Zance ya kare: Sanata Yari ya fadi abu 1 da za a tallata Tinubu da shi a Najeriya

Source: Facebook
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na NDC, Osa Director, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 10 ga watan Satumban 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.
Kotu ta yanke hukunci kan sabon tambarin
Mai Shari’a J.O. Abdulmalik ne ya yanke hukuncin, bayan da NDC ta shigar da ƙara kan batun tambarin jam’iyyar.
NDC ta zargi INEC da cire sabon tambarinta daga bayanan hukumar, tare da maye gurbinsa da tsohon tambarin ƙungiyar da jam’iyyar ta fara rajista da shi.
Lamarin ya zo ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027, inda tambura da kayan kamfen ke taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan magoya baya.
NDC ta ce INEC ta cire sabon tambarin
A cewar Osai Director, taron farko na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na NDC da aka gudanar ranar 25 ga Maris, 2026, ya amince da sabon tambarin.
Ya ce daga bisani jam’iyyar ta aika da tambarin ga INEC domin a saka shi cikin bayanan hukumar.
Osai Director ya ce INEC ta fara ɗora sabon tambarin a bayananta, amma daga baya ta cire shi tare da mayar da tsohon tambarin ba tare da sanar da jam’iyyar wani ingantaccen dalili ba.
Jam’iyyar ta garzaya kotu
NDC ta ce da farko ta yi ƙoƙarin warware matsalar ta hanyar tattaunawa da INEC da kuma hanyoyin gudanarwa, jaridar TheCable ta kawo labarin.
Sai dai, a cewar jam’iyyar, ta yanke shawarar zuwa kotu ne bayan hukumar ta gaza yin gyaran da ta nema.
A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Abdulmalik ta umarci INEC da ta amince da sabon tambarin NDC, ciki har da alamarsa da launukansa, domin amfani da jam’iyyar a hukumance.
Kotun ta hana INEC tsoma baki
Kotun ta kuma bayar da umarnin dindindin da ya hana INEC dakatarwa ko tsoma baki wajen amfani da alamar nasara mai yatsu biyu da NDC ta ƙirƙira a matsayin tambarinta.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, Osai Director ya ce kotun ta kawo ƙarshen takaddamar da ta shafi tambarin jam’iyyar.
Ya ce saboda haka, an umarci ’yan takara da mambobin NDC da su fara amfani da sabon tambarin da kotu ta amince da shi nan take a kan kayan kamfen da sauran kayayyakin jam’iyya.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa zai mayar da litar fetur N200, ya fadi abin da ya shirya

Source: Getty Images
NDC za ta nemi gudunmawa don kamfe
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta bayyana hanyar da za ta tattara kudaden yakin neman zaben 2027.
Jam'iyyar NDC ta ce za ta nemi gudummawar kuɗi daga talakawan Najeriya domin rage tasirin masu hannu da shuni a tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.
Asali: Legit.ng
