Ta Faru Ta Kare: INEC Ta Shirya Sanar da Makomar Takarar Sheikh Pantami a Zaben 2027

Ta Faru Ta Kare: INEC Ta Shirya Sanar da Makomar Takarar Sheikh Pantami a Zaben 2027

  • Hukumar INEC za ta tattauna muhimman batutuwan da suka shafi zaɓen 2027, ciki har da cancantar wasu 'yan takarar gwamna
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, ne zai jagoranci taron manema labarai da taron masu ruwa da tsaki a Abuja ranar Talata, 6 ga Oktoba
  • Hukuncin Kotun Ƙoli kan wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 ya haifar da fassarori daban-daban tsakanin jam'iyyu da 'yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Alamu sun nuna cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) za ta yi bayani kan muhimman batutuwan da suka shafi babban zaɓen 2027 a ranar Talata mai zuwa.

Ana sa ran daga cikin abubuwan da INEC za ta yi bayani a mako mai zuwa har da tambayoyin da suka shafi cancantar wasu 'yan takarar gwamna.

Kara karanta wannan

'Dan Najeriya ya ciri tuta, ya zama shugaban hukumar WAEC ta Yammacin Afirka

INEC.
Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Hukumar INEC za ta dauki matsaya

Leadership ta ce da yiwuwar hukumar za ta tattauna batutuwan ne a wani taron manema labarai na duniya da taron masu ruwa da tsaki da za a gudanar a Abuja ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2026.

An shirya taron ne domin cika kwanaki 100 kafin a kada kuri'a ta farko a babban zaɓen 2027, kuma shugaban hukumar, Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, ne zai jagoranci taron.

INEC ta gayyaci jam'iyyun siyasa, kafafen yaɗa labarai, hukumomin tsaro, ƙungiyoyin fararen hula, shugabannin addinai, abokan hulɗa, mambobin ƙungiyar diflomasiyya da sauran masu ruwa da tsaki zuwa taron.

'Yan takarar da ake magana a kansu

Daga cikin 'yan takarar da ake shakku kan takararsyakwai Hon. Kingsley Chinda, ɗan takarar gwamna na APC a jihar Rivers da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ɗan takarar gwamna na PDP a jihar Gombe.

Sauran sun hada da tsohon babban sufeton 'yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, ɗan takarar gwamna na SDP a jihar Nasarawa da Abdulrahman Bashir Haske, ɗan takarar gwamna na APM a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Baya lashe zabe, Pantami ya sako APC a gaba, ya ce zai bi su har gida muhawara

Matsayin 'yan takarar ya jawo muhawara daga jam'iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kwanan nan kan wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.

Ana sa ran INEC za ta yi bayani

Wata majiya daga hukumar INEC ta shaida cewa INEC na iya bayyana matsayinta kan hukuncin Kotun Ƙoli bayan kammala nazarinsa a taron manema labarai na ranar Talata.

Majiyar ta ce hukumar tana nazarin hukuncin, kuma taron zai ba ta damar bayyana matsayinta ga jam'iyyun siyasa, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki.

“Tabbas, INEC za ta yi magana kan wannan muhimmin batu da wasu batutuwa ranar Talata. Ƙungiyar lauyoyinmu ta gabatar da rahotonta kan batun, kuma na tabbata shugaban hukumar zai yi magana a kai a wannan rana,” in ji majiyar.

Dokokin da kotun koli ta dawo da su

A ranar 24 ga Satumba, 2026, Kotun Ƙoli ta maido da tanade-tanade huɗu na Dokar Zaɓe ta 2026 waɗanda a baya Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke.

Tanade-tanaden, wato sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2), sun fi mayar da hankali kan rajistar mambobin jam'iyyun siyasa da kuma tsaida 'yan takara.

Kara karanta wannan

An sanya sabon lokacin yanke hukunci a shari'ar sojojin da suka yi yunkurin kifar sa Tinubu

Pantami.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan da dan takarar gwamnan PDP a jihar Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: INEC Nigeria, Prof. Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Sashe na 77(5) ya shafi rajistar mambobin jam'iyya da za a yi amfani da ita wajen gudanar da zaɓen fidda gwani.

Tun bayan hukuncin, an samu fassarori daban-daban tsakanin jam'iyyun siyasa da 'yan takarar da tarihin siyasarsu ya haɗa da sauya sheka daga wata jam'iyya zuwa wata.

Pantami ya shirya yin muhawara

Kun ji cewa dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa ya shirya yin muhawara da sauran 'yan takara gabanin zaben 2027.

Ya kara da cewa duk wanda yaki zuwa muhawara dole za a bi shi har gida domin ya fito ya bayyanawa al'ummar jihar Gombe manufofinsa kafin ya shugabance su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262