Dan Takarar Sanata Ya Kwanto Kura kan Matsalar Tsaro, Ya Nemi Tinubu Ya Yi Murabus

Dan Takarar Sanata Ya Kwanto Kura kan Matsalar Tsaro, Ya Nemi Tinubu Ya Yi Murabus

  • Dan takarar sanata na APMz Olufemi Ajadi Oguntoyinbo ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus kan tabarbarewar tsaro
  • Ya kuma bukaci Tinubu ya janye daga neman wa’adi na biyu a 2027 idan gwamnatinsa ta kasa magance matsalolin tsaro
  • Ajadi ya ce dole gwamnati ta fifita ceto matasa masu yi wa kasa hidima, NYSC 19 da aka yi garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, Jihar Oyo - Dan takarar sanatan APM a mazabar Oyo ta Tsakiya, Ambasada Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus kan tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Ajadi ya kuma bukaci Tinubu ya janye daga neman wa'adi na biyu a 2027 idan gwamnatinsa ta kasa magance matsalolin tsaron da ke addabar ’yan Najeriya.

Bol Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Yan bindiga sun sace matsan NYSC

Kara karanta wannan

Iyaye sun shiga ha’ula’i, ‘yan bindiga sun bukaci N950m kafin sakin masu NYSC

Vanguard ta ruwaito cewa ya yi wannan kiran ne yayin da yake mayar da martani kan rahoton sace matasa 19 da ake shirin tura wa aikin yi wa kasa hidima (NYSC).

An ce matasan na tafiya daga Ibadan a Jihar Oyo zuwa sansanonin horas da su na NYSC da ke jihohin Abia da Akwa Ibom lokacin da masu garkuwa suka sace su.

Rahotanni sun ce ’yan bindiga sun yi garkuwa da matasan ne bayan sun kai hari kan motocin bas biyu a kan hanyar Owerri-Onitsha da ke Umunoha a Jihar Imo ranar Alhamis.

Dan takarar sanata ya maida martani

Ajadi ya bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, musamman ganin cewa wadanda abin ya shafa matasan Najeriya ne da ke tafiya domin shiga shirin yi wa kasa hidima.

“Abin dariya ne kuma rashin hankali ne a ce ’yan NYSC da ke tafiya domin yi wa kasarsu hidima an yi garkuwa da su.
“Waɗannan matasa ’yan Najeriya ne da suka kammala karatunsu, kuma ana tura su ne domin su ba da gudunmawa wajen ci gaban kasarsu,” in ji shi.

Kara karanta wannan

'Babban abin da zai raba Bola Tinubu da mulkin Najeriya a 2027'

Dan takarar na APM ya bukaci Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen gano tare da ceto ’yan NYSC din da aka yi garkuwa da su.

Ajadi ya nemi Tinubu ya yi murabus

Ajadi ya kuma nuna damuwa kan rahoton cewa masu garkuwar sun bukaci a biya N50m a matsayin fansa kan kowane mutum daga cikin 19, wanda zai kai N950m idan adadin da aka ruwaito ya kasance daidai.

Ya ce ya kamata gwamnati ta dauki matakan karfafa tsaro a manyan hanyoyin da ’yan NYSC da sauran ’yan Najeriya ke amfani da su wajen tafiya tsakanin jihohi.

“Idan ba a iya ceto wadannan ’yan NYSC ba, to y kanata shugaban kasa ya yi murabus. Bai dce shugaban kasa, wanda yake uba ga kasa, ya ci gaba da gudanar da aikinsa yayin da wasu daga cikin ’ya’yansa ke hannun yan ta'adda ba,” in ji shi.

Tinubu ya roki karin lokaci daga yan Najeriya

Kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na kokarin gyara kurakuran da aka tara a karkashin gwamnatocin da suka gabata.

Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su kara bai wa gwamnatinsa dama domin ta kammala ayyukan da ta fara, yana mai cewa zaman lafiya na dawowa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262