Peter Obi Ya Kinkimo Maganar Kisan Sardauna, Ya Bayar da Shawara

Peter Obi Ya Kinkimo Maganar Kisan Sardauna, Ya Bayar da Shawara

  • Peter Obi ya ce Najeriya za ta iya samun sauyi mai yawa cikin shekaru huɗu idan aka ba shi damar jagorantar ƙasar bayan zaɓen 2027
  • Obi ya bayyana rashin tsaro a matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin ƙasar, yana mai cewa ya hana manoma zuwa gona da masana’antu jigilar kayayyaki
  • Ɗan takarar ya kuma yi magana kan kisan da aka yi wa Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello, lokacin juyin mulkin shekarar 1996

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya ce ’yan Najeriya za su ga babban sauyi cikin shekaru huɗu idan aka ba shi damar shugabantar ƙasar bayan zaɓen 2027.

Peter Obi ya bayyana cewa zai yi kokarin magance matsalar rashin tsaron da ta addabi Najeriya.

Obi ya yi magana kan kisan Sardauna
Peter Obi na yin jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 10 ga watan Satumban 2026 yayin wata hira da tashar Arise TV, inda ya yi magana kan halin da ƙasar ke ciki, rashin tsaro, farashin man fetur, cin hanci da kuma shirinsa na mulki.

Kara karanta wannan

"A wasu lokutan," Ana zargin ba Shugaba Tinubu ke tafiyar da mulkin Najeriya ba

Obi ya ce bai san abubuwan da suka faru a baya ba

Da yake mayar da martani kan tambayar da aka yi masa game da kisan Sardaunan Sokoto, Obi ya ce ya yi ƙanƙanta a lokacin da wasu daga cikin abubuwan da ake magana a kansu suka faru.

“Ni yaro ne lokacin da duk waɗannan abubuwan suka faru,” in ji shi.

Ya ce ya kamata ’yan Najeriya su daina mayar da hankali kan rikice-rikicen baya, su maida hankali wajen gina ƙasa mai haɗin kai.

A cewarsa, Najeriya za ta iya shawo kan matsalolin da suka addabe ta ta hanyar “ƙauna, haɗin kai da ci gaba”.

Ya yi alƙawarin kawo sauyi cikin shekaru huɗu

Obi ya bayyana kwarin gwiwar cewa idan aka ba shi damar jagorantar ƙasar, za a fara ganin gagarumin sauyi cikin shekaru huɗu.

“Cikin shekaru huɗu, mutane za su ga bambancin,” in ji shi.

Ya ce ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatinsa za ta fara mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Dan takara ya yi alkawarin samar da lantarki a kowane gida cikin watanni 11 a Najeriya

Obi ya ce rashin tsaro ya durƙusar da tattalin arziki

Obi ya bayyana rashin tsaro a matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta a yanzu.

Ya ce matsalar ta yi illa ga harkokin tattalin arziki, musamman saboda masana’antu na fuskantar matsala wajen jigilar kayayyaki, yayin da manoma ke kasa zuwa gonakinsu cikin aminci.

“Tsaro shi ne abu mafi muhimmanci ga ’yan Najeriya. Rashin tsaro ya sa masana’antu ba sa iya jigilar kayayyaki. Haka kuma ya hana manoma zuwa gona,” in ji shi.

Ya ce saboda haka, tabbatar da tsaron ƙasa zai kasance abin da gwamnatinsa za ta fara fifitawa idan aka zaɓe shi.

Ya yi alƙawarin rage farashin fetur

Da yake magana kan tsadar man fetur, Obi ya ce zai mayar da hankali wajen kawar da cin hanci da rashawa da kuma matsalolin rashin inganci da ke cikin tsarin tallafin man fetur.

A cewarsa, yin hakan zai taimaka wajen rage farashin man fetur da sauran kayayyaki.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki da yan sanda suka tabbatar da hari kan ayarin motocin Peter Obi

“Zan kawar da cin hanci a cikin tallafin man fetur. Idan na kawar da shi, farashin fetur da komai zai ragu. A yanzu muna sayen man fetur da tsada,” in ji shi.

Obi ya kuma ce kasancewar Najeriya ƙasa mai arzikin man fetur ya kamata ya sa gwamnati ta sarrafa albarkatun man yadda ya kamata domin amfanin ’yan ƙasar.

Obi ya ce zai inganta Najeriya
Peter Obi na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Peter Obi ya yabi Makinde

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa takwaransa na jam'iyyar adawa ta APM kuma gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya cancanci zama shugaban Najeriya.

Peter Obi ya ce bai kamata neman shugabancin Najeriya ya kasance bisa son rai ko gaba tsakanin 'yan siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng