Abdulaziz Yari na Hada kan Jama'a, Baraka Ta Barke a APC a Zamfara
- Jigon jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Hajiya Hadiza Liman, ta fice daga jam’iyyar tare da magoya bayanta zuwa jam'iyyar NDC
- Hadiza ta ce ta koma NDC ne saboda zargin cewa Gwamna Dauda Lawal ya yi watsi da ita da magoya bayanta duk da irin goyon bayan da suka ba shi
- Ta ce za ta mara wa ɗan takarar gwamnan NDC, Sanata Kabiru Garba Marafa, baya tare da magoya bayanta a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara – Jigon jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Hajiya Hadiza Liman, ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar tare da magoya bayanta zuwa jam’iyyar NDC.
Ta bayyana matakin ne yayin da take zantawa da manema labarai a gidanta da ke Gusau ranar Juma’a, inda ta ce magoya bayanta daga ƙananan hukumomi 14 na jihar sun bi ta zuwa sabuwar jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta

Source: Facebook
Dalilin Hadiza na fita daga APC
Tribune ta rahoto cewa Hadiza Liman ta ce ta ɗauki matakin ne saboda zargin cewa Gwamna Dauda Lawal ya yi watsi da ita da magoya bayanta bayan sun ba shi cikakken goyon baya lokacin da yake jam’iyyar PDP.
Ta ce ta bi Lawal daga PDP zuwa APC ne bayan ya koma jam’iyyar, amma daga bisani ta ce gwamnan ya kasa kula da su.
“Tun da muka bi Gwamna Dauda Lawal daga PDP zuwa APC, Gwamna Dauda Lawal ya kasa kula da mu,”
In ji Hadiza Liman.
Rahoton ya ce Hadiza Liman ta bayyana cewa sama da magoya baya 5,000 daga ƙananan hukumomi 14 ne suka koma NDC tare da ita.
Wanda za ta zaba a 2027
Hadiza Liman ta bayyana fatan cewa NDC da ɗan takararta na gwamna, Sanata Kabiru Garba Marafa, za su samu nasara a zaɓen gwamnan Zamfara na 2027.
Rahoton Leadership ya nuna cewa Hadiza ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su mara wa Marafa baya a zaɓen da ke tafe.

Source: Original
Hadiza ta soki gwamnatin Zamfara
Jigon ta kuma bayyana wasu dalilan da suka sa ta fice daga APC, ciki har da abin da ta bayyana a matsayin rashin girmama ofishin majalisar malaman addinin Musulunci ta jihar.
Ta yi zargin cewa an mayar da ofishin majalisar zuwa wani wuri tare da ware tsohon ofishin ga matar gwamnan.
Liman ta kuma yi kira ga malaman addinin Musulunci a jihar da su daina goyon bayan Gwamna Dauda Lawal tare da komawa NDC.
APC ta caccaki Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa magoya bayan Shugaba Bola Tinubu ƙarƙashin ƙungiyar Tinubu Must Stay (TMS) sun mayar da martani ga kiran ’yan adawa na neman a sauya gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027.
Kungiyar ta ambaci karuwar tattalin arziki, shirin rancen karatu na NELFUND da sauya motoci zuwa amfani da CNG cikin abubuwan da ta ce ya kamata a duba yayin muhawarar siyasar 2027.
TMS ta ce sauye-sauyen gwamnatin Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur da sauye-sauyen kasuwar canjin kudin waje, sun kawo sauyi duk da matsalolin da suka haifar.
Asali: Legit.ng
