'Neman Fitina Yake Yi': Gwamnatin Benue Ta Yi Martani Mai Zafi bayan Jifan Peter Obi
- Gwamnatin Benue ta zargi Peter Obi da neman tayar da hankali, bayan da aka toshe ayarin motocinsa yayin ziyararsa jihar a ranar Talata
- Kwamishinan Yaɗa Labarai, Solomon Iorpev, ya ce Obi bai sanar da gwamnatin jihar a hukumance kafin ziyarar ba, wanda ya saba ka’idojin aiki
- Iorpev ya ce ba a san mutanen da suka toshe ayarin ba, yana mai cewa ziyarar Obi ta zo daidai da taron matasan ƙananan hukumomi 23
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Gwamnatin Benue ta caccaki dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi bayan iftila'in da ya faru da shi a jihar.
Gwamnatin ta zargi Peter Obi, wanda ke takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), da neman tayar da hankali.

Kara karanta wannan
Halin da ake ciki da yan sanda suka tabbatar da hari kan ayarin motocin Peter Obi

Source: UGC
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Solomon Iorpev, ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan cikas da aka yi wa ayarin motocin Obi yayin ziyararsa jihar ranar Talata, cewar Punch.
'Kuskuren da Peter Obi ya yi'
Iorpev ya ce ya kamata Obi ya sanar da gwamnatin jihar a hukumance kafin zuwansa, yana mai bayyana hakan a matsayin keta ƙa’idar aiki, kamar yadda Daily Post ta ce.
Kwamishinan ya ce kasancewar Obi tsohon gwamnan jiha ne kuma fitaccen ɗan siyasa, gwamnati na da alhakin shirya isasshen tsaro domin kare shi.
“Ana sa ran mu tabbatar da tsaronsa da kariyarsa, amma a halin da babu wasiƙar da aka aiko, ba za mu iya tabbatar da tsaron nasa ba.
“Wannan ba shi ne karo na farko da yake yin hakan ba. Kawai yana neman tayar mana da hankali ne. Mu mutane ne masu son zaman lafiya da karɓar baƙi."

Source: Original
Abin da ake zargin ya jawo rigimar
Iorpev ya ce bai san mutanen da suka toshe ayarin motocin Obi ba, amma ya ƙara da cewa ziyarar ta zo daidai da wani taron matasa wanda ake yi a jihar.
Ya ce taron ya ƙunshi matasa daga dukkan ƙananan hukumomi 23 na Benue, lamarin da ka iya kasancewa dalilin cunkoson hanyar yayin da ayarin Peter Obi ke wucewa.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Saboda haka, idan suna zuwa ne daga Tarka, Gboko, Buruku, Ushongo, Konshisha ko Vandeikya a daidai lokacin da ya kai ziyarar, suka toshe hanya, abin takaici ne. Ban san matasan da suka yi hakan ba."
Kwankwaso ya magantu bayan hari kan Obi
A wani labarin, mun ba ku rahoto cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi Allah-wadai da tare ayarin Peter Obi yayin da yake kan hanyar zuwa Benue, yana bayyana lamarin a matsayin barazana ga dimokuraɗiyya.
Tsohon gwamnan na Kano ya bukaci gwamnatin Benue ta tabbatar da tsaron Obi da tawagarsa, tare da ba su damar gudanar da zirga-zirga cikin ’yanci.
Masu zanga-zanga sun tare hanyar Gboko a Makurdi, suna rera “Ba ma son Peter Obi,” lamarin da ya hana ayarinsa ci gaba da tafiya.
Asali: Legit.ng
