An Cafke Hafsat kan Zargin Yaɗa Rahoton Cewa Opay Za Su Bar Najeriya
- Rundunar yan sanda sun cafke wata mata bisa zargin ƙirƙira da yaɗa takardar bogi da ke cewa kamfanin fintech OPay zai daina aiki
- Yan sanda sun ce binciken kwararru ya gano asalin labarin ƙarya zuwa wani shafin sadarwa da ake zargin Abubakar ce ke sarrafa shi
- Rundunar ta ce har yanzu ana ci gaba da bincike, tare da ƙara jajircewa wajen yaƙi da laifukan intanet da yaɗa bayanan ƙarya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta samu nasarar cafke wata da ake zargin ta yada karya kan kamfanin Opay.
Rundunar ta cafke Hafsat Abubakar da ake zargi da ƙirƙira da yaɗa takardar bogi da ke cewa wani kamfanin fintech zai daina aiki.

Source: UGC
Rahotanni sun bayyana cewa wani labari ya bazu a makon da ya gabata, inda aka yi ikirarin cewa OPay, babban kamfanin fintech, zai daina aiki, cewar Premium Times.
Labarin ya kuma gargadi kwastomomin kamfanin da su cire kuɗaɗensu kafin ranar 1 ga Satumba, saboda zargin dakatar da ayyukan kamfanin.
Sanarwar da Opay ta fitar an jita-jitar
Sai dai OPay ta fitar da sanarwa a shafinta da Legit Hausa ta samu, inda ta karyata labarin tare da bayyana cewa “ƙarya ne.”
A wani taron manema labarai da aka shirya domin fayyace lamarin, Babban Lauyan OPay, Akinfolabi Moses, ya ce ’yan sanda da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) suna binciken lamarin.

Source: Twitter
An cafke wacde ake zargi kan yada karya
Kakakin ’yan sanda, Ani Iniedu, ya bayyana a wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba cewa an cafke Hafsat Abubakar bayan binciken kwararru.
A cewar Channels TV, Iniedu ya ce binciken ya gano asalin labarin zuwa wani asusun X da Hafsat ke gudanarwa.
Ya bayyana cewa an cafke wadda ake zargin ne ranar 4 ga Satumbar shekarar 2026 da muke ciki.
OPay ta taba gano wasu asusun X guda biyu, inda ta ce ta rubuta musu tare da bukatar su cire labarin da suka wallafa, cewar Punch.
Sai dai ba a bayyana ko ɗaya daga cikin waɗannan asusun yana da alaƙa da wadda aka cafke ba, duk da haka, kakakin ’yan sandan ya ce bincike na ci gaba.
Ya sake jaddada ƙudurin rundunar na yaƙi da laifukan intanet, ciki har da yaɗa bayanan ƙarya da ka iya rage amincewar jama’a ga kamfanoni da hukumomi.
Gwamnati ta fara karbar haraji gun masu Opay
A baya, an ji cewa Gwamnatin tarayya ta fara cin N50 kan duk wani kudi da aka turawa masu amfani da bankunan intanet da ya haura N10,000.
Tuni dai bankunan intanet irinsu Opay da Moniepoint suka bayyana cewa sun fara cajar kudin kuma za su tura su kai tsaye ga hukumar FIRS.
Wasu masu sana'ar POS da 'yan kasuwa da muka zanta da su, sun nemi gwamnati da ta janye wannan haraji da iya tsanantawa talaka duk da halin da ake ciki.
Asali: Legit.ng

