Shugaban APC zai Yi Aiki da Bindigar AK 47 kan Masu Adawa da Tinubu

Shugaban APC zai Yi Aiki da Bindigar AK 47 kan Masu Adawa da Tinubu

  • Shugaban jam'iyyar APC na jihar Edo, Jarrett Tenebe, ya ambaci amfani da bindigar AK-47 yayin da yake magana kan shirin jam'iyyar na samar da kuri'u miliyan 2.5 ga Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
  • Tenebe ya ce Gwamna Monday Okpebholo ya yi alkawarin cewa Edo za ta bai wa Tinubu kuri'u miliyan 2.5, yana mai cewa jam'iyyar za ta yi aiki domin ganin an cimma wannan buri
  • Shugaban APC din ya yi wannan magana ne a wani taron magoya bayan jam'iyyar a Benin City bayan zaben kananan hukumomin jihar, inda ya ce APC ta samu kuri'u 2,158,600 a zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Benin City – Shugaban APC na jihar Edo, Jarrett Tenebe, ya yi magana kan matakin da zai dauka ga mutanen da yake ganin za su yi yunkurin hana jam'iyyar cimma burinta na samar da kuri'u miliyan 2.5 ga Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: INEC ta shirya sanar da makomar takarar Sheikh Pantami a zaben 2027

Tenebe ya yi wannan magana ne a ranar Juma'a a Benin City yayin da yake jawabi ga magoya bayan APC a wani taron jam'iyyar da aka gudanar bayan zaben kananan hukumomin jihar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shirin samar da kuri'u miliyan 2.5

The Cable ta rahoto cewa Tenebe ya ce Gwamna Monday Okpebholo ya yi wa Tinubu alkawarin cewa jihar Edo za ta samar masa da kuri'u miliyan 2.5 a zaben shugaban kasa na 2027.

Ya ce APC za ta yi aiki domin tabbatar da cewa ta cimma wannan adadi, inda ya danganta hakan da sakamakon da jam'iyyar ta ce ta samu a zaben kananan hukumomin jihar.

Tenebe ya yi ikirarin cewa APC ta samu kuri'u 2,158,600 a zaben kananan hukumomin, yana mai bayyana adadin a matsayin wani abu da bai taba faruwa a wata jiha ba.

Tenebe ya ambaci AK-47

Da yake magana kan mutanen da yake ganin za su iya kawo cikas ga shirin jam'iyyar, Tenebe ya ambaci amfani da bindiga.

Ya ce:

“Masu rashin fatan alheri a gare mu, wadanda suke son kawo mana cikas, ina yi muku addu'a.”

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Ranar yanci: Atiku ya ɗauko batun da yan Najeriya ke buƙata sani kan raba tallafin N75,000

“Duk wanda ya ki, wanda yake son tsayawa a kan hanyarmu domin hana mu samun kuri'un da muke son bai wa Shugaban kasa, AK-47 za ta yi aiki.”

Maganar Tenebe ta zo ne yayin da ake samun wasu kalamai masu alaka da barazana daga wasu 'yan siyasa gabanin babban zaben 2027.

Ga bidiyon bayanin da ya yi da Leadership ta wallafa a X:

Shugaban APC na kasa
Shugaban APC, Farfesa Nentawe na bayani a wajen taro. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Gargadin jigon APC a Borno

A wani labarin, kun ji cewa Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Borno, Sainna Buba, ya yi gargadi ga masu sukar gwamnatin Gwamna Babagana Zulum.

Buba ya ce duk wanda ya daga yatsa yana adawa da gwamnati, za a “yanke masa yatsa”, yayin da yake magana a wani taron yakin neman zabe da City Boy Movement, kungiyar da ke goyon bayan neman wa Tinubu wa'adi na biyu.

Sainna Buba ya yi kalaman ne a Maiduguri a wani taron kaddamar da yakin neman zaben da City Boy Movement ta shirya domin nuna goyon baya ga wa'adin shugaba Tinubu na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng