"A Wasu Lokutan," Ana Zargin ba Shugaba Tinubu ke Tafiyar da Mulkin Najeriya ba

"A Wasu Lokutan," Ana Zargin ba Shugaba Tinubu ke Tafiyar da Mulkin Najeriya ba

  • Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi ya yi zsrgin cews wasu lokutan da kamar ba Shugaba Bola Tinubu ke da cikakken iko kan gwamnatinsa ba
  • Ya ce rashin tsaro shi ne babban kalubalen da ’yan Najeriya ke fuskanta kuma zai ba da fifiko wajen magance shi idan ya zama shugaban ƙasa
  • Tsohon gwamnan Anambra ya ce zai naɗa ƙwararrun shugabannin hukumomin tsaro a makon farko na mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya ce akwai lokutan da yake ganin ba Shugaba Bola Tinubu ba ne ke da cikakken iko kan gwamnatinsa ba.

Obi ya ce ya kamata shugaban kasa da kansa ya riƙa yi wa ’yan Najeriya bayani kan batutuwan da suka shafi ƙasar, maimakon barin mataimakansa da abokansa su riƙa magana a madadinsa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ware gwamna a Arewa ya kwararo masa yabo

Peter Obi.
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Peter Obi, @aonanuga1956
Source: Twitter

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da Arise TV ranar Alhamis, inda ya yi magana kan halin da ƙasar ke ciki, rashin tsaro, farashin man fetur, cin hanci da rashawa da kuma shirinsa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.

Obi ya nemi Tinubu ya rika magana

Peter Obi ya ce:

“Wani lokaci ina ganin Tinubu ba shi ke mulkin kasar nan ba. Duk waɗannan abubuwan da mutanensa ke faɗa, shi ya kamata ya kasance yana faɗarsu
“Babu wanda zai yi magana a madadin Peter Obi. Ni zan yi wa mutanena magana,” in ji shi

Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya kuma yi tambaya kan yawan tafiye-tafiyen Shugaban Ƙasar zuwa ƙasashen waje, yana mai cewa ya kamata ya fi mayar da hankali wajen ziyartar sassan Najeriya da rashin tsaro ya addaba.

Ya ce Tinubu ya kamata ya ziyarci jihohi irin su Zamfara, Sokoto, Plateau da Kano domin ya ga halin da ake ciki na tsaro da idonsa.

Kara karanta wannan

Tinubu bai cire kansa ba, ya faɗi irin shugabannin da Najeriya ke buƙata

Rashin tsaro shi ne babban matsala

Obi ya bayyana rashin tsaro a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ’yan Najeriya ke fuskanta, yana mai cewa lamarin ya yi matuƙar shafar harkokin tattalin arziki a faɗin ƙasar.

Ya ce rashin tsaro ya sanya masana’antun cikin mawuyacin hali wajen jigilar kayayyaki, yayin da manoma suka kasa zuwa gonakinsu cikin aminci.

“Tsaro shi ne abu mafi muhimmanci ga ’yan Najeriya. Dhi yasa ba zai yiwu masana’antun su kai kayayyakinsu inda ake buƙata ba. Rashin tsaro ya sanya ba zai yiwu manoma su je gona ba,” in ji shi.

Obi ya ce saboda haka, tabbatar da tsaron ƙasa zai kasance babban abin da gwamnatinsa za ta fara mayar da hankali a kai idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.

Obi Peter.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Peter Obi ya dauki alkawari

Tsohon gwamnan ya ce zai fara sake fasalin tsarin tsaro tun daga makon farko na mulkinsa ta hanyar naɗa ƙwararrun shugabannin hukumomin tsaro.

Ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da dukkan albarkatun da ake da su da kuma fasahar zamani wajen yaƙi da rashin tsaro, ciki har da jirage marasa matuƙa da tauraron ɗan adam wajen sanya ido.

Kara karanta wannan

"Na samu labari mara dadi"; Atiku ya haska matsalar da matasa ke fuskanta a gwamnatin Tinubu

Obi zai kawo hanyar tattara sakamako

Kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya ce tawagarsa za ta samar da tsarin aika sakamakon zaɓe kai tsaye daga rumfunan zaɓe.

Ya ce abin da yake son yi shi ne tabbatar da cewa kowace rumfar zaɓe tana da tsarin da zai aika da ingantaccen sakamakonta zuwa cibiyar tattara bayanan tawagarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262