‘Su Suke Kawo Kansu’: Pantami kan ’Yan TikTok da ke Barinsa zuwa Jamilu

‘Su Suke Kawo Kansu’: Pantami kan ’Yan TikTok da ke Barinsa zuwa Jamilu

  • Ɗan takarar gwamnan PDP a Gombe, Isa Ali Pantami, ya ce bai damu da rushe zaɓen da kotu ta yi ba
  • Pantami ya yi ikirarin cewa mutane ne ke zuwa gare shi , yana cewa gwamnati kan tallafa wa waɗanda suka samu kusanci da shi
  • Tsohon ministan ya ce Allah ya yi masa baiwa, yana mai cewa ’yan siyasa suna kwaikwayon ayyukansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Pantami, Gombe - Dak takarar gwamnan PDP a jihar Gombe, Isa Ali Pantami ya yi magana bayan nasarar lashe zaben fitar da gwani.

Pantami ya ce bai damu ba ko kadan bayan kotu ta rusa zaben da aka yi a baya, ya ce ya godewa Allah da samun nasara.

Pantami ya dura kan gwamnatin APC a Gombe
Dan takarar APC, Jamilu Isiyaku Gwamna yayin ba shi takara a Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Ismaila Uba Misilli, Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani bidiyo da DCL Hausa ta wallafa a Facebook wanda wakilin Legit Hausa ya bibiya a yau Lahadi.

Kara karanta wannan

An zo wajen: An fara shirin daina kai shanu daga Arewa zuwa Kudu

A cikin bidiyon, Pantami ya ce kowane dan siyasa na neman al'umma amma shi fa mutane su suke zuwa gare shi saboda tasirinsa.

Ya ce"

"Duk da siyasa ana neman kowa da kowa, wanda kika gani a wurinmu su suke kawo kansu wurinmu, mu mun fuskanci talakawa ne da ke gida za su yi dangwale.
"Ai ba ni na je wurinsu ba, su suka zo gida ko ofis saboda mu gana, mu muna jin dadin haka saboda gwamnati ba ta taimakon jama'a sai wanda ya zo kusa da mu.
"Idan ka dauki hoto da ni, gwamnati za ta neme ka, idan muka yi taro na dauki hoto da wani, ina yin hoton domin samar 'da aiki ko tallafi, saboda gwamnati za ta kira ka, ta baka N500,000 ko miliyan 1, ai kin ga na tallafi miki.
"Duk wanda ya wallafa hotonsa da ni yana cewa Gombe sai Malam, yanzu za a kira ka sai a tallafa maka, ko baka siyasa za a neme ka."

Kara karanta wannan

Amaechi ya fayyace saukin da za a samu tun shekarar farko idan Atiku ya kafa gwamnati

Pantami ya godewa Allah bayan nasara a zaben fitar da gwani
Dan takarar jam'iyyar PDP, Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Twitter

'Baiwar da Allah ya yi mani' - Pantami

Pantami ya ce shi Allah ya yi masa baiwa, komai da ya yi gwamnati na kwaikwayonsa saboda ya zama tauraro.

"Dalili kuma shi ne babu abin da zan koya a gare su amma su kuma kullum koyon abubuwa suke yi daga gare ni.
"Mun zama taurari a karatun addini na zamani da aikin gwamnati, shiyasa muke kiransu yan siyasa ne da ke koyi da duk abin da muka yi.
"Ko ta'aziyya na je na dan jam'iyya ta sai ka ga sai an kwaikwaya, hakan yana sa komai muka yi sai sun shiga sai kwaikwaya."

- Cewar Pantami

Wani masoyin APC ya yi martani

AbdulRahman Dawaki ya ce ko kadan babu mai kwaikwayonsa saboda shi ne ma sabon yanka a siyasar jihar Gombe.

Ya ce idan ka duba shekarun da Jamilu Gwamna ya yi yana siyasa zai tabbatar da maka da cewa ba za ka taba hada su ba.

Kara karanta wannan

'Da Bello Turji ne da tuni sun sake shi': Malami kan tsare Nnamdi Kanu a Sokoto

Ya ce:

"Jamilu Gwamna ba sa'ansa ba ne duba da shekarun da ya kwashe yana siyasa, a lokacin da ya fara neman takara, babu labarin Pantami."

Pantami ya kalubalanci yan takara a Gombe

Mun ba ku labarin cewa dan takarar jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa ya shirya yin muhawara da sauran 'yan takara.

Hakan na zuwa ne bayan sake gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP da aka yi bayan hukuncin kotu saboda rikicin cikin gida.

A bayanin da ya yi, Panntami ya yi zargin cewa wasu 'yan takara sun fara rokon kar a shirya muhawarar domin kaucewa yin abin kunya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.