Shugaba Tinubu Ya Ware Gwamna a Arewa Ya Kwararo Masa Yabo

Shugaba Tinubu Ya Ware Gwamna a Arewa Ya Kwararo Masa Yabo

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ta ya gwamnan Zamfara Dauda Lawal murnar cika shekara 61 a duniya
  • Bola Tinubu ya ce gwamnatin Dauda Lawal ta gyara fiye da makarantu 800, ta ɗauki malamai sama da 2,000 tare da inganta asibitoci
  • Shugaban ƙasar ya taya Dauda Lawal murnar cika shekaru 61, tare da yi masa fatan samun lafiya da ƙarin ƙarfi wajen yi wa jama’ar Zamfara hidima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a matsayin “gwamnan Renaissance” saboda sauye-sauyen da ya ce gwamnan ya kawo a jihar.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin saƙon taya Lawal murnar cika shekaru 61 da haihuwa, inda ya yaba wa gwamnatinsa kan ayyukan raya kasa da samar da ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu bai cire kansa ba, ya faɗi irin shugabannin da Najeriya ke buƙata

Tinubu ya yabi Dauda Lawal
Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Dauda Lawal, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya a shafinsa na X.

Shugaban ƙasar ya kuma jinjina wa gwamnatin Dauda Lawal kan shirye-shiryen farfaɗo da birane da kuma ƙoƙarin bunƙasa masana’antu a jihar Zamfara.

An gyara makarantu sama da 800

A cikin sanarwar wadda mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya kuma bayyana wasu nasarorin gwamnatin Lawal a fannonin ilimi da lafiya.

Ya ce gwamnatin jihar ta gyara tare da farfaɗo da fiye da makarantu 800 a faɗin Zamfara.

Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatin ta ɗauki malamai sama da 2,000 aiki domin ƙarfafa harkar koyarwa da inganta ilimi a jihar.

A fannin lafiya kuwa, shugaban ƙasar ya ce an inganta wasu asibitoci tare da samar da kayan aikin lafiya da sauran kayayyakin amfani na asibiti a sassan jihar.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Abin da zai faru da masu zagi da sukar gwamnatin Tinubu

Bola Tinubu ya yabi salon mulkin Dauda Lawal

Shugaban ƙasar ya ce yadda Gwamna Dauda Lawal ke gudanar da mulki a fannoni daban-daban na da matuƙar muhimmanci wajen samun ci gaba mai ɗorewa.

Ya ce irin wannan tsarin na taimakawa wajen samun ci gaba a fannoni daban-daban, musamman wajen bunƙasa ci gaban ɗan Adam.

“Shugaba Tinubu na taya Dr Dauda Lawal murna a wannan lokaci, yana mai bayyana shi a matsayin gwamnan Renaissance wanda ya kawo sauyi mai kyau a Zamfara,” in ji sanarwar.

Tinubu ya taya gwamnan murnar cika shekaru 61

Tinubu ya yi wa Gwamna Dauda Lawal fatan samun ƙoshin lafiya da ƙarin ƙarfi yayin da yake ci gaba da yi wa al’ummar Zamfara hidima.

Ya kuma bayyana fatan cewa gwamnan zai ci gaba da ba da gudunmawarsa wajen ci gaban jihar da Najeriya baki ɗaya.

Shugaban ƙasar ya bi sahun iyalan Dauda Lawal, abokansa da al’ummar jihar Zamfara wajen taya gwamnan murnar cika shekaru 61 da haihuwa a duniya.

Kara karanta wannan

Ana batun zaben 2027, Kwankwaso ya aika sako kan makomar Najeriya

Shugaba Tinubu ya taya Dauda Lawal murna
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tarayyar Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Akpabio ya bukaci a goyi bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman matasan Arewa.

Shugaban Majalisar Dattawan ya bukace su da su goyi bayan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng