Gwamnonin Arewa 6 Sun Yi Taro, Sun Mika Muhimmiyar Bukata ga Tinubu
- Gwamnonin Arewa maso Gabas sun nemi a farfaɗo da ayyukan binciken man fetur da suka tsaya a Magumeri da Gubio na jihar Borno
- NEGF ta yaba wa Shugaba Tinubu kan farfaɗo da aikin haƙar mai na Kolmani da wasu manyan ayyukan sufuri a yankin
- Gwamnonin sun kuma nemi a ƙara zuba jari a ilimi, samar da ayyukan yi ga matasa da inganta tsaro da haɗin kan jihohin yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta farfaɗo da ayyukan binciken man fetur da suka tsaya a wasu sassan jihar Borno.
Gwamnonin sun ce ya kamata a sake duba ayyukan da aka fara a ƙananan hukumomin Magumeri da Gubio, amma daga baya suka tsaya.

Source: Facebook
Mataimakin Shugaban NEGF kuma Gwamnan Adamawa, Rt. Hon. Umaru Fintiri, ne ya karanta sanarwar da ƙungiyar ta fitar bayan taronta na 13 da aka gudanar a Maiduguri, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
An gudanar da taron na kwanaki biyu tsakanin 2 zuwa 3 ga Oktoba, 2026, inda gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe suka tattauna kan tsaro, tattalin arziki da ayyukan more rayuwa.
NEGF ta yaba wa Tinubu kan aikin Kolmani
Gwamnonin sun nuna matuƙar godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa sabunta kulawar Gwamnatin Tarayya ga wasu muhimman ayyukan raya Arewa maso Gabas.
Sun yaba musamman kan farfaɗowar aikin hakar man fetur na Kolmani da ke jihar Gombe, tare da sauran manyan ayyuka a yankin.
Daga cikin ayyukan akwai layin dogo na Port Harcourt–Jos–Bauchi–Gombe–Maiduguri da babbar hanyar Akwanga–Jos–Bauchi–Gombe–Biu–Maiduguri.
Gwamnonin sun jaddada haɗin kan yankin
NEGF ta ce haɗin kai tsakanin gwamnonin jihohin shida shi ne ɗaya daga cikin manyan nasarorin da ta samu cikin shekaru shida da suka gabata.
An kafa ƙungiyar ne a taronta na farko da aka gudanar a Gombe a watan Maris na 2020.
Gwamnonin sun ce haɗin kan ya ba yankin damar magana da murya ɗaya da kuma tura manufofin da suka haifar da wasu ci gaba, jaridar The Punch ta kawo labarin.
An mayar da hankali kan samar da wutar lantarki
A fannin makamashi, gwamnonin sun yaba wa jihohin yankin bisa ƙoƙarin samar da tsari na bai ɗaya kan makamashi.
Sun ambaci tashar samar da wutar lantarki ta Dadinkowa, wadda a yanzu ke samar da wuta ga babban layin ƙasa.
Sun kuma ƙarfafa jihohin da su yi amfani da sabuwar dokar wutar lantarki da kuma yawan hasken rana da ake samu a yankin wajen faɗaɗa ƙananan tashoshin samar da wuta.

Source: Facebook
Gwamnonin sun kuma sake yin kira da a gaggauta kammala aikin tashar samar da wutar lantarki ta Mambila, wanda ya daɗe yana fuskantar tsaiko.
Sun ce an samu ci gaba bayan warware wasu matsalolin shari’a da suka dabaibaye aikin sakamakon hukuncin sasantawa.
An bukaci Tinubu ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa an takarar sanatan APM a mazabar Oyo ta Tsakiya, Ambasada Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus kan tabarbarewar tsaro a Najeriya.
Ajadi ya kuma bukaci Tinubu ya janye daga neman wa'adi na biyu a 2027 idan gwamnatinsa ta kasa magance matsalolin tsaron da ke addabar ’yan Najeriya.
Asali: Legit.ng

