Gwamna Ya Fallasa Mutanen da ke Taimakon Masu Hakar Ma'adanai ba Bisa Ka'ida ba

Gwamna Ya Fallasa Mutanen da ke Taimakon Masu Hakar Ma'adanai ba Bisa Ka'ida ba

  • Gwamna Agbu Kefas ya ce gwamnatin Taraba ba za ta ƙara bari a kwashe albarkatun ma’adanai ba tare da bin ƙa’idojin gwamnati ba
  • Kefas ya zargi wasu jami’an gwamnati da jami’an tsaro da taimakawa ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a wasu sassan jihar
  • Gwamnatin jihar ta shirya samar da kayan aiki da bayanai masu inganci domin taimaka wa masu haƙar ma’adinai na gaskiya su yi aiki bisa doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, ya yi barazanar rushe wata hanyar da ake zargin tana taimaka wa ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta ƙara amincewa da amfani da albarkatun ma’adanai na jihar ba tare da bin tsarin doka da ƙa’idojin da gwamnati ta gindaya ba.

Kara karanta wannan

Fasto ya je Isra'ila bayan korafin kisan Kiristoci, ya yi addu'a ga Netanyahu

Gwamna Kefas ya yi jawabai
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas a ofis Hoto: Agbu Kefas
Source: Twitter

Gwamna Kefas ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 3 ga watan Oktoban 2026 yayin ganawa da kananan masu haƙar ma’adanai a Jalingo, jaridar Leadership ta kawo rahoton.

Ya zargi wasu jami’ai da hannu

Gwamnan ya zargi wasu jami’an gwamnati da jami’an tsaro da hannu wajen taimaka wa ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa hakan na da alaƙa da matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan jihar.

Ya ce matsalar ba ta tsaya ga masu haƙar ma’adanai da ke aiki a wurare masu nisa kawai ba.

A cewarsa, wasu mutane da ke cikin hukumomin gwamnati sun zama wani ɓangare na hanyar da ake zargin tana tafiyar da ayyukan harƙallar ma’adanai.

“Mun fi samun haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba daga cikin mutanen da ke gwamnati fiye da waɗanda ke waje,” in ji Kefas.

Za a samar da tsarin aikin masu hakar ma’adanai

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa na son fahimtar yadda wannan tsarin harƙallar yake, domin ta magance shi ta hanyar ƙara haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, masu kula da harkokin ma’adanai da kuma al’ummomin masu haƙar ma’adinai.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi maganar hana hawa a Kano bayan kalaman bangaren Aminu Ado

Ya ce gwamnati za ta samar da wani tsari da zai bai wa masu haƙar ma’adanai na gaskiya damar gudanar da ayyukansu bisa doka.

Hakan, a cewarsa, zai kuma sauƙaƙa wa hukumomin gwamnati gano tare da ɗaukar mataki kan waɗanda ke kwashe albarkatun jihar ba bisa ka’ida ba.

Gwamnati za ta taimaka da kayan aiki

Kefas ya umarci ƙungiyar masu haƙar ma’adanai da ta gabatar da cikakken jerin kayan aikin da mambobinta ke buƙata, tare da bayyana kiyasin kuɗin da za a kashe wajen samunsu.

Ya ce gwamnati za ta nemi hanyoyin samun tallafin kuɗi domin sayen kayan aikin tare da rarraba su zuwa wuraren da aka ware domin aikin haƙar ma’adanai.

A cewarsa, masu haƙar ma’adinai da aka yi wa rajista kuma aka samar musu da kayan aiki yadda ya kamata za su gudanar da ayyukansu a wuraren da gwamnati ta amince da su.

Haka kuma, za a ƙarfafa masu sayen ma’adinai su rika sayen kayayyakin ne daga wuraren da aka tsara, domin inganta bin diddigin inda ma’adinai suka fito da kuma sa ido daga gwamnati.

Kara karanta wannan

An fara murna da gwamnatin Tinubu ta cika alkawarin da ta daukarwa sojojin Najeriya

Gwamna Kefas ya yi maganar masu hakar ma'adanai
Taswirar jihar Taraba, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masi hakar ma'adanai sun mutu a Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa akalla masu hakar ma’adanai tara sun mutu bayan ambaliyar ruwa ta mamaye wani ramin da suke hakar ma’adanai a Bauchi.

Lamarin mara dadi ya auku ne a ƙauyen Nahuta, Gundumar Gwana, ƙaramar hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng