Rigima Sabuwa: An Sake Kai Hari Mai Zafi a Saduiyya
- Houthi sun ce sun kai hari kan wata cibiyar man fetur ta Aramco kusa da Riyadh da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa
- Wuta da hayaki mai yawa sun tashi daga matatar man fetur ta Aramco a ranar Asabar, amma ba a bayyana musabbabin gobarar ba
- Ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ya yi watsi da ikirarin Houthi, yana mai cewa bayanin ƙungiyar yaudara ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Riyadh, Saudiyya - Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta yi ikirarin cewa ta kai hari kan wata babbar cibiyar man fetur a Saudiyya da makamai masu linzami masu cin dogon zango da jirage marasa matuƙa.
Ikirarin ya zo ne bayan an ga wuta da wani babban hayaƙi na tashi daga matatar man fetur ta Aramco a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan
Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta

Source: Getty Images
Rahoton tashar Aljazeera ya ce jami’an kashe gobara sun shiga aikin kashe gobarar da ta tashi a wurin.
Houthi ta yi ikirarin kai hari Saudiyya
Sai dai hukumomin Saudiyya da kamfanin Aramco ba su fitar da sanarwar gaggawa da ke bayyana musabbabin gobarar ba.
Houthi sun danganta harin da hare-haren sama Yahya Saree, kakakin Houthi, ya ce a wani saƙo da ya wallafa a shafin X cewa hare-haren sun haddasa gobara a wuraren da aka kai wa hari.
Ya ce an kai hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren sama da Saudiyya ke kai wa yankunan Yemen da Houthi ke iko da su, ciki har da babban birnin ƙasar, Sanaa.
Saree ya kuma yi ikirarin cewa an kai hare-haren sama kusan 60 kan yankunan da Houthi ke iko da su cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Sai dai har yanzu ba a samu tabbaci mai zaman kansa kan waɗannan ikirare ba.
Ƙawancen Saudiyya ya musanta ikirarin
A gefe guda, ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta wajen yaƙi da Houthi a Yemen ya yi watsi da ikirarin cewa ƙungiyar ta kai hari kan babban birnin Saudiyya, Riyadh.
Manjo-Janar Turki al-Malki, kakakin ƙawancen, ya bayyana ikirarin Houthi a matsayin “yaudara” a wata hira da kafar Asharq Al-Awsat.
Ya ce Houthi na ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a daga abin da ya kira girman asarar da ƙungiyar ta yi da kuma ƙara nuna fushin jama'a a kanta.
An yi ikirarin asarar mayaƙan Houthi a Taiz
Al-Malki ya kuma ce abin da Houthi ke fuskanta a Taiz, da kuma asarar rayukan mambobinta a hannun dakarun sojin Yemen da ƙungiyar Popular Resistance, na sa ƙungiyar neman bayyana nasarorin da ba su tabbata ba.
A baya, Houthi sun ce sun kai hari da makami mai linzami da jirgi mara matuƙi kan wata cibiyar man fetur ta Aramco kusa da Riyadh.
Ƙungiyar ta kuma ce harin ya haddasa babbar gobara a wurin. Sai dai har zuwa lokacin da rahoton ya fito, hukumomin Saudiyya da Aramco ba su bayyana a hukumance musabbabin gobarar ba.

Source: Getty Images
An kai hari a Madina
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar haɗin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta ta zargi mayakan Houthi da kai hari kan wata tashar rarraba wutar lantarki a birnin Madina da ke Saudiyya.
Harin ya shafi tashar Taibah da ke samar da wutar lantarki ga Masallacin Annabi SAW, inda ɗaya daga cikin na’urorin sauya wuta ya fita daga aiki ba tare da katse tsarin wutar lantarki ba.
Asali: Legit.ng

