Maganin Magudi: Obi Ya Kawo Sabuwar Hanyar Tattara Sakamakon Zaben 2027
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya ce tawagarsa za ta samar da tsarin aika sakamakon zaɓe kai tsaye daga rumfunan zaɓe
- Obi ya ce tsarin zai gudana ne tare da hanyar isar da sakamakon da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ke amfani da ita, domin bai wa tawagarsa damar sa ido
- Tsohon gwamnan Anambra ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa sakamakon ya fito daga rumfunan zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana shirin da yake son aiwatarwa domin sa ido kan sakamakon zaɓe a babban zaɓen 2027.
Obi ya ce tawagarsa za ta kafa tsarin da zai aika sakamakon da aka tattara sakamako daga kowace rumfar zaɓe zuwa cibiyar tattara bayananta.

Kara karanta wannan
Dan takara ya yi alkawarin samar da lantarki a kowane gida cikin watanni 11 a Najeriya

Source: Twitter
Arise TV ta rahoto cewa Obi ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da gidan talabijin ɗin ranar Alhamis.
Ya ce tsarin zai kasance ne tare da hanyar da INEC za ta yi amfani da ita wajen aika sakamakon zaɓe.
Ya ce:
“Dole ne mu tabbatar cewa a kowace rumfar zaɓe an ƙidaya kuri'u, an rubuta su yadda ya kamata, sannan an aika da su yadda ya kamata.
“Za mu kuma samar da hanyar aika sakamakon sau biyu, ta yadda yayin da ake aikawa da shi zuwa shafin INEC da aka tanada, za a kuma aika da shi zuwa inda mutane za su iya gani.”
Karin bayani daga Obi
Da aka tambaye shi ko shirin samar da ƙarin tsarin IReV a faɗin ƙasar yana nufin kafa wata hanyar aika sakamako ta daban, Obi ya ce ba haka ba ne.
Ya ce abin da yake son yi shi ne tabbatar da cewa kowace rumfar zaɓe tana da tsarin da zai aika da ingantaccen sakamakonta zuwa cibiyar tattara bayanan tawagarsa.

Source: Facebook
“Abin da muke cewa shi ne a wannan karon, za mu tabbatar cewa a kowace rumfar zaɓe akwai tsarin da zai aika da ingantaccen sakamakon da aka samu zuwa cibiyar tattara bayananmu,”
In ji shi.
Tsohon gwamnan Anambra ya kuma ce za a iya gudanar da zaɓe cikin gaskiya da riƙon amana, yana mai kawo Ghana da wasu ƙasashe a matsayin misali.
Keyamo ya kare Peter Obi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su daina yada labaran da ke nuna son zuciya wajen rahoton rikicin siyasa.
Keyamo ya yi wannan kiran ne bayan rahotannin da suka bayyana cewa an tare Peter Obi a jihar Benue, inda ya ce ya kamata 'yan siyasa su samu damar gudanar da kamfen ba tare da tsoratarwa ko tashin hankali ba.
An rahoto cewa wasu matasa sun hana Obi zuwa Yelwata da ke ƙaramar hukumar Guma a jihar Benue, inda ya shirya ziyartar iyalan waɗanda harin da aka kai a yankin a watan Yunin 2025 ya shafa.
Asali: Legit.ng
