2027: Peter Obi Ya Bayyana Gwamna 1 da Ya Cancanci Zama Shugaban Kasar Najeriya
- Dan takarar shugaban kass na NDC, Peter Obi ya bayyana cewa dan takarar APM, Seyi Makinde, ya cancanci zama shugaban Najeriya
- Tsohon gwamnan Anambra ya ce siyasa bai kamata ta zama ta gaba da juna ko neman mulki ta kowane hali ba
- Obi ya ce zai goyi bayan duk wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2027 cikin adalci da gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa takwaransa na jam'iyyar adawa ta APM kuma gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya cancanci zama shugaban Najeriya.
Obi ya bayyana hakan ne ranar Litinin a wajen kaddamar da ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na Makinde da ke Abuja.

Source: Twitter
Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Anambra ya yi kira ga 'yan siyasa su hada kai gabanin babban zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan
Gwamna ya yi barazana ga sarakunan gargajiya kan shiga siyasa, ya fadi abin da zai faru da su
Obi ya yabawa Makinde
Peter Obi ya ce bai kamata neman shugabancin Najeriya ya kasance bisa son rai ko gaba tsakanin 'yan siyasa ba.
A cewarsa, ya kamata babban burinsu ya zama gina Najeriya mai inganci da kyakkyawar makoma ga al'ummarta.
Ya ce:
"Muna son Najeriya ta zama kasa mai hadin kai da bai wa kowa dama. Muna da dan takara da yake neman zama shugaban kasa a yau, dan uwana Makinde. Shin ya cancanci zama shugaban kasa? Eh, ya cancanta."
Obi zai goyi bayan wanda ya yi nasara
Dan takarar shugaban kasar ya kuma yi alkawarin goyon bayan duk wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2027, kamar yadda Punch ta kawo.
Obi ya ce:
"Abin da muke yi a yau, a wajenmu, ba batun son rai ko neman mulki ta kowane hali ba ne, muna son 'yan Najeriya su zabi wanda suke so.
"Dole ne dukkanmu mu hada kai wajen gina sabuwar Najeriya. Ba za mu iya ci gaba da tafiya a wannan hanyar ba, mutanenmu suna fama da yunwa da talauci.

Kara karanta wannan
2027: An samu gwamna na farko da ya goyi bayan tsarin Atiku na rage tsadar fetur a Najeriya
"Duk wanda ya yi nasara ta gaskiya a zabe mai 'yanci, adalci da sahihanci, za mu hada kai domin ceto kasar nan daga durkushewa."
Obi ya nemi a sauya salon siyasa
Peter Obi ya bukaci 'yan siyasa su daina mayar da hankali kan sabani tsakaninsu da kuma gaba. Ya ce ya kamata su karkata karfinsu wajen magance matsalolin da 'yan Najeriya ke fuskanta.
A cewarsa, dalilin da ya sa ya halarci taron kaddamar da yakin neman zaben Makinde shi ne domin nuna goyon baya da kuma karfafa sabon salon siyasa.

Source: Facebook
Obi ya ce Najeriya na bukatar shugabannin siyasa da za su fifita jin dadin 'yan kasa a kan bukatunsu na kashin kai ko na jam'iyya.
Ya jaddada cewa ya kamata a bai wa 'yan Najeriya damar zabar shugaban kasar da suke so cikin 'yanci.
Peter Obi ya shirya mutuwa a zaben 2027
Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Nigeria NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa a shirye yake ya rasa ransa domin kare kuri'unsa a zaben 2027.
Obi ya bukaci 'yan Najeriya da su tabbatar ba a sake maimaita maguɗan zaben da aka gani a lokacin babban zaben shekarar 2023 ba.
Asali: Legit.ng