Tinubu Bai Cire Kansa ba, Ya Faɗi Irin Shugabannin da Najeriya ke Buƙata
- Shugaba Bola Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su zabi shugabannin da za su fifita muradun jama’a da ci gaban ƙasa kan son kai
- Tinubu ya bayyana hakan ne yayin bikin godiya na cika shekaru 70 na tsohon SGF, Boss Mustapha, a cocin LCCN da ke Jimeta, Yola
- Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana Boss Mustapha a matsayin abin koyi wajen gaskiya a hidimar gwamnati, tare da kira ga haɗin kan shugabannin siyasar Arewa ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jimeta, Adamawa — Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya bayyana irin shugabannin da suka dace da kasar yayin da ake shirin zaben shekarar 2027.
Tinubu ya yi kira ga shugabanni da ’yan ƙasa masu kishin ƙasa, wadanda za su fifita amfanin jama’a kan muradun kansu wajen neman ci gaban ƙasa.

Source: Facebook
Tinubu ya yi wannan kiran ne a Jimeta, Yola, yayin wani taron godiya na bikin cika shekaru 70 na tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Dakta Boss Mustapha, cewar Vanguard.
Shawarar da Tinubu ya ba yan ƙasa
Shugaban ya samu wakilcin SGF, Sanata George Akume, inda ya bukaci jami’an gwamnati da ’yan ƙasa su mayar da sadaukarwa ga hidimar jama’a da amfanin kowa a matsayin muhimmiyar daraja.
Ya ce Najeriya na bukatar shugabannin da za su kasance masu jagoranci bisa muradun da suka wuce neman ci gaban kansu.
Ya ce:
“Yau da farko rana ce ta yin godiya. Mun taru ba wai kawai don murnar cika shekaru 70 ba, har ma don murnar amincin Ubangiji, wanda ya kiyaye tare da tallafa wa Boss Mustapha a matakai daban-daban na rayuwarsa.
“Najeriya na bukatar maza da mata wadanda ke daraja abin da ya wuce muradun kansu, maimakon haka su kasance masu sadaukar da kansu ga hidimar jama’a."
Abin da gwamnan Plateau ya ce a taron
Da yake nasa jawabin, Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya bayyana Mustapha a matsayin abin koyi wajen nuna gaskiya da rikon amana a hidimar gwamnati.
Mutfwang ya kuma yi kira da a kara samun haɗin kai tsakanin shugabannin siyasa a yankin Arewa ta Tsakiya domin samun ci gaba.
Haka kuma, Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda mataimakinsa, Farfesa Kaletapwa George Farauta, ya wakilta, ya yaba wa tsohon SGF saboda gudunmawarsa wajen gina ƙasa da kuma jajircewarsa a hidimar jama’a.
Taron godiyar ya samu halartar shugabannin siyasa, jami’an gwamnati, ’yan uwa, abokai da sauran masu fatan alheri domin murnar cika shekaru 70 na Mustapha.
'Babu batun cafke Tinubu a Amurka'
Mun ba ku labarin cewa Jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce Shugaba Tinubu ba zai fuskanci kamu ba a Amurka.
Ya ce yarjejeniyar 1947 tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Amurka ta kare shugabannin ƙasashe da iyalansu wanda hakan zai kare shugaban daga cafke shi.
Ibrahim ya bayyana cewa zargin aikata laifi kaɗai bai isa a hukunta mutum ba, domin dole ne a tabbatar da zargin ta hanyar doka.
Asali: Legit.ng

