Malamin Musulunci Ya Tsage Gaskiya kan Batun Malamai 500 Sun Goyi bayan Tazarcen Tinubu

Malamin Musulunci Ya Tsage Gaskiya kan Batun Malamai 500 Sun Goyi bayan Tazarcen Tinubu

  • Sheikh Abdurrahman Azzamfari ya ce rahoton cewa malamai 500 sun amince da sake zaɓen Tinubu a 2027 ba gaskiya ba ne
  • Ya bayyana cewa taron Muslim Intellectual Forum an gabatar musu da shi ne a matsayin wani dandali na ba da shawara ga gwamnati
  • Malamin ya ce idan gwamnati na son goyon bayansu, ya kamata ta saurari shawarwarinsu kuma ta aiwatar da su a zahiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wani fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Abdurrahman Abubakar Azzamfari, ya musanta cewa malamai 500 daga jihohin Arewa sun amince da sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Malamin ya bayyana cewa ikirarin da aka yi bayan wani taron ‘Muslim Intellectual Forum’ da aka gudanar a Dutse, Jihar Jigawa, ba gaskiya ba ne. Azzamfari ya ce ba a tattauna batun Tinubu ba.

Kara karanta wannan

VeryDarkMan: Dan Tiktok ya nuna wa 'yan sanda tsaurin ido bayan sun gayyace shi

Azzamfari ya yi magana kan Tinubu
Sheikh Abdurrahman Abubakar Azzamfari da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Sheikh Azzamfari Tv, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sheikh Azzamfari ya yi wannan bayani ne a wani faifan bidiyo da ya yaɗu a shafin sada zumunta na Facebook.

Malamin ya ce batun amincewa da sake zaɓen Tinubu bai kasance cikin abubuwan da mahalarta taron suka amince da su ba.

“Maganar cewa malamai 500 da suka halarci taron sun amince da Tinubu kuma suka ce za su sake zaɓensa ba gaskiya ba ce. Ba a tattauna hakan da mu ba sam.”

Malamin ya kuma musanta cewa mahalarta taron sun bai wa Shugaban ƙasa “goyon baya dari bisa ɗari” kan neman wa’adi na biyu.

A cewarsa, idan da gaske ne ake son malaman su mara wa Tinubu baya, da farko ya kamata gwamnati ta saurari shawarwarinsu tare da aiwatar da su.

Ya bukaci a rubuta duk wata yarjejeniya

Sheikh Azzamfari ya ce idan gwamnati na son samun goyon bayan malaman, ya kamata ta saurari ra’ayoyinsu da shawarwarinsu sannan ta tabbatar da an aiwatar da su.

Kara karanta wannan

An shiga yanayin tashin hankali da bam ya tashi da mutane a jihar Zamfara

Ya kuma bayyana cewa duk wata yarjejeniya da za a cimma tsakanin malaman da gwamnati ya kamata a rubuce take kuma a bai wa mahalarta kwafin abin da aka amince da shi.

Ya ce hakan zai ba su damar sanin abin da gwamnati ta ɗauka a matsayin alkawari kafin su fito su mara mata baya a fili.

An gabatar da taron ba da sunan siyasa ba

Azzamfari ya bayyana cewa taron na Jigawa shi ne karo na biyar da aka shirya tun bayan fara tarukan Muslim Intellectual Forum a watan Afrilu.

Ya ce ya halarci taruka uku daga cikin biyar, ciki har da wanda aka gudanar a Abuja, taron Kaduna na uku da kuma na baya-bayan nan a Dutse.

A cewarsa, an zaɓi malamai 12 daga kowace jiha ta Arewa domin halartar taron Jigawa, kuma dukkaninsu sun isa wurin lafiya tare da komawa gidajensu lafiya.

Malamin ya ce tun farko an gabatar musu da dandalin ne a matsayin wani taro da ba shi da alaƙa da siyasa, wanda manufarsa ita ce taimaka wa gwamnati da kuma tallafa wa al'umma.

Kara karanta wannan

Abin mamakin da Bashir El Rufa'i ke gani idan ya ziyarci babansu da ke tsare

Ya yi zargin an yi amfani da sunansu

Azzamfari ya ce an kuma gaya musu cewa za su ba gwamnati shawara kan kurakuran da take yi da hanyoyin da za a gyara su.

Sai dai ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda aka gudanar da taron a Jigawa. Ya ce an bar mahalarta suna jira daga ƙarfe 11:00 na safe har zuwa bayan ƙarfe 2:30 na rana kafin gwamnoni da wasu jami'an gwamnati su fara magana.

A cewarsa, bayan gwamnoni sun yi jawabi, an fitar da 'yan jarida daga wajen taron. Daga baya, an sake kiran 'yan jaridar cikin taron, inda aka sanar da su cewa malaman sun amince da sake zaɓen Tinubu a 2027.

“An yi kamar ana wasa da mu”

Sheikh Azzamfari ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya, yana mai cewa yadda aka gudanar da taron ya sa ya zama kamar ana wasa da malamai a gaban gwamnoni da manyan jami'an gwamnati.

Ya ce daga cikin sama da malamai 500 da suka halarci taron, malami ɗaya kacal daga Kano aka ba damar yin magana na tsawon mintuna biyu, sannan aka dakatar da shi.

Kara karanta wannan

'Ba da yawun Musulmin Najeriya ba': ADC ta soki Malamai kan neman a zabi Tinubu

Malamin ya jaddada cewa abin da ya faru ba ya wakiltar matsayar dukkan malaman da suka halarci taron, kuma bai kamata a danganta su da wata sanarwar goyon bayan siyasa da ba su amince da ita ba.

Azzamfari ya yi magana kan Tinubu
Sheikh Abdurrahman Abubakar Azzamfari Hoto: Sheikh Azzamfari Tv
Source: Facebook

Hanyar tallata Tinubu a zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Abdulaziz Abubakar Yari, ya ce matasan Najeriya za su kasance masu matuƙar muhimmanci wajen isar da sakonnin jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

Yari ya ce matasa za su taka muhimmiyar rawa wajen isar da manufofi da abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cimma a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda zuwa ga al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng