Kasar Musulunci Ta Iran Ta Sake Kafa Tarihi a Duniya Tana ciki Yaki da Amurka

Kasar Musulunci Ta Iran Ta Sake Kafa Tarihi a Duniya Tana ciki Yaki da Amurka

  • Kasar Musulunci ta Iran ta sake shiga gaban kasashen duniya wajen gani rijiyoyin hako gas mafi yawa a shekarar 2026
  • Iran ta samu mafi yawan sababbin wuraren samar da gas da aka gano a duniya tun daga 2025, inda adadin da aka gano a rijiyoyin Takht da Pazan ya kai ƙafa cubic tiriliyan 17.5
  • Rijiyar iskar gas ta Takht da ke kudancin lardin Fars ta ƙunshi ƙafa cubic tiriliyan 7.5 na iskar gas, wanda ake hasashen za a iya hako ƙafa cubic tiriliyan 5.5

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Iran ta sake shiga gaban Amurka da sauran kasashen duniya wajen samun mafi yawan sababbin wuraren samar da iskar gas da aka gano a duniya tun daga shekarar 2025.

Alkaluma sun nuna cewa jimillar iskar gs da aka gano a rijiyoyin Takht da Pazan na kasar Musulunci ta Iran ta kai ƙafa cubic tiriliyan 17.5.

Kara karanta wannan

Ana zargin Gwamnatin Najeriya ta shiga yarjejeniyar sulhu da Boko Haram a asirce

Iran.
Shugaban kasar musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Rahoton TV BRICS da aka fitar ranar Alhamis, 10 ga watan Satjmba, 2026, abokin hulɗar kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ne ya bayyana hakan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Adadin ya ƙunshi iskar gas da aka gano a rijiyoyin biyu tun daga farkon shekarar 2025, abin da ya sanya Iran ta zama ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan sabuwar iskar gas da aka gano a wannan lokacin.

Iran za ta fadada binciken fetur

Iran ta shirya faɗaɗa ayyukan binciken man fetur da iskar gas saboda dimbin albarkatun hydrocarbon da take da su.

A cewar rahoton, wani ɓangare na ƙarfin binciken Iran zai mayar da hankali ne kan yankunan Arewa maso Gabas, Arewa da Arewa aso Yammacin ƙasar.

An tsara faɗaɗa ayyukan ne domin taimakawa wajen ci gaba da bincike da gano wasu ƙarin albarkatun hydrocarbon a sassa daban-daban na Iran.

Iran, wadda ta fuskanci yaƙi da Amurka tun watan Fabrairun 2026, na shirin faɗaɗa ayyukan binciken albarkatun ƙasa saboda dimbin damar da take da ita ta fuskar hydrocarbon.

Kara karanta wannan

‘Dan takarar shugaban kasa a PRP ya ce gara mulkin soja da tsarin yau

Jaridar ICIR ta ruwaito cewa binciken ya sanya Iran gaba da sauran ƙasashe wajen yawan sababbin rijiyoyin haƙo iskar gas da aka gano a wannan lokaci, kamar yadda jami’an Iran suka bayyana.

Matatar mai.
Daya daga cikin masana'antun tace mai da gas na kasar Iran Hoto: Chain
Source: Facebook

Iran na da gas mai yawa

Tuni Iran ta kasance ƙasa ta biyu a duniya wajen yawan tabbatattun ma’adinan iskar gas, inda aka kiyasta tana da tiriliyan 1,200 cubic feet har zuwa watan Disamban 2023, a cewar Hukumar Kula da Makamashi ta Amurka.

Ƙasar ta mallaki kusan kashi 16 cikin 100 na tabbatattun ma’adinan iskar gas na duniya, sannan ita ce ƙasa ta uku a duniya wajen samar da busasshiyar iskar gas a 2022.

Rasha da China na tre da Iran

A wani labarin, kun ji cewa mambobin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) sun gudanar da kuri'ar mika batun nukiliyar Iran zuwa ga Kwamitin Tsaron UN.

An amince da wannan kuduri ne bayan samun kuri'u 23 daga kasashe mambobi, yayin da kasashe uku suka ƙi amincewa, sannan kasashe takwas suka janye jikinsu.

Kasashen Rasha, China da Nijar ne suka kaɗa kuri'ar ƙin amincewa da kudurin wanda kasashen Biritaniya, Faransa, Jamus da Amurka suka gabatar gaban kwamitin gudanarwa na hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262