Zance Ya Kare: Sanata Yari Ya Fadi Abu 1 da Za a Tallata Tinubu da Shi a Najeriya
- APC ta ce kamfen ɗinta na 2027 zai kasance kan batutuwa da ayyukan da gwamnatin Tinubu ta aiwatar, maimakon kai wa ’yan siyasa hare-hare
- Abdulazeez Yari ya ce ’yan Najeriya sun ci gaba da nuna kishin ƙasa tare da kare haɗin kan Najeriya duk da matsalolin da ƙasar ta fuskanta
- Yari ya ce ganawarsa ta farko a matsayin shugaban kwamitin kamfen da sarakunan gargajiya na da muhimmanci wajen samun goyon bayansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Shugaban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC ya bayyana hanyar tallata Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Sanata Abdulaziz Yari ya bayyana cewa cewa kamfen ɗinsa na zaɓen 2027 zai kasance kan batutuwa da nasarorin gwamnati, ba wai kai wa wasu mutane hari ba.

Source: Twitter
Sanata Abdulazeez Yari, ya bayyana hakan ne a Gusau bayan kammala wata ganawar sirri da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da sarakunan gargajiya a jihar ranar Laraba, 9 ga watan Satumban 2026, cewar rahoton tashar Channels tv.
APC za ta yi kamfen kan ayyukan gwamnati
Yari ya ce kamfen ɗin APC na 2027 zai mayar da hankali kan abubuwan da jam’iyyar ta yi da kuma abin da take shirin yi idan aka sake ba ta damar jagorantar ƙasar.
Ya ce Najeriya ta fuskanci lokuta masu wahala da dama waɗanda suka sanya wasu ke tunanin ko ƙasar za ta ci gaba da kasancewa ɗaya.
Sai dai ya ce duk da irin waɗannan ƙalubale, ’yan Najeriya sun ci gaba da nuna jajircewarsu wajen tabbatar da haɗin kan ƙasar.
“Najeriya ƙasa ce mai ban mamaki. Mun ga abubuwa da dama da wasu suka yi hasashen cewa Najeriya ba za ta ci gaba da kasancewa ƙasa ɗaya ba, tun daga 12 ga Yuni da sauran abubuwa. Amma ga inda muke yanzu. ’Yan Najeriya suna ci gaba da tabbatar da cewa ƙasar nan ta kasance ɗaya,” in ji Yari.
Yari ya yaba wa Tinubu
Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya ce Shugaba Bola Tinubu ya himmatu wajen kawo ci gaban Najeriya, yana mai cewa shugaban na ƙaunar ƙasar.
“Tinubu ya fi ƙarfin kowane mutum. Yana tare da ’yan Najeriya, kuma shi shugaba ne da ke ƙaunar wannan ƙasa ba tare da wata tantama ba,” in ji shi.
Yari ya ce kamfen ɗin 2027 ba zai kasance na yin sabbin alkawura kawai ba, sai dai nuna wa ’yan Najeriya ayyukan da gwamnatin APC ta riga ta cimma.
Ya nemi goyon bayan sarakunan gargajiya
Yari ya ce ganawarsa ta farko a hukumance tun bayan naɗa shi shugaban kwamitin kamfen ita ce da sarakunan gargajiya.
Ya ce duk da cewa sarakunan gargajiya ba ’yan siyasa ba ne, suna da kusanci da jama’a kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da al’umma.
A cewarsa, neman goyon baya da albarkar sarakunan gargajiya na da matuƙar muhimmanci ga nasarar kamfen ɗin APC a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Yari ya magantu kan dawo da tallafin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya yi fatali da yunkurin dawo da tallafin mai.
Sanata Yari ya bayyana cewa duk wanda zai fito ya yi wa ’yan Najeriya alkawarin dawo da tallafin man fetur yana yaudararsu kawai.
Asali: Legit.ng

