An ga Tashin Hankali da Mutane Sama da 20 Suka Mutu bayan Kwankwadar Maganin Gargajiya

An ga Tashin Hankali da Mutane Sama da 20 Suka Mutu bayan Kwankwadar Maganin Gargajiya

  • Akalla mutane 24 sun mutu a Odigbo da Araromi-Obu bayan sun sha wani maganin gargajiya da ake zargin yana da alaƙa da mutuwar
  • Shugaban ƙaramar hukumar Odigbo ya ce mutane takwas sun mutu a Araromi-Obu, yayin da 16 suka mutu a garin Odigbo
  • ’Yan sanda da Ma’aikatar Lafiya ta Ondo sun fara bincike, suna gargadin jama’a da kada su yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ondo - Akalla mutane 24 sun mutu a wasu garuruwa biyu da ke ƙaramar hukumar Odigbo a jihar Ondo, bayan sun sha wani maganin gargajiya.

Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun suma kafin daga bisani su mutu a wurare daban-daban.

Mutane sama da 20 sun mutu a Ondo
Taswirar jihar Ondo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahoton jaridar TheCable ya nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar, 5 ga Satumba, a garin Odigbo da kuma Araromi-Obu.

Kara karanta wannan

Jirgin sama dauke da ma'aikatan lafiya ya gamu da hatsari dukkan mutanen ciki sun mutu

Mutane da dama na kwance a asibiti

Wasu mazauna yankunan da suka sha ruwan maganin sun kuma samu matsala, inda ake ci gaba da ba su magani a asibitoci daban-daban.

Shugaban ƙaramar hukumar Odigbo, Taiwo Adegoroye, ya tabbatar da mutuwar mutane 24. Ya ce mutane takwas sun mutu a Araromi-Obu, yayin da wasu 16 suka mutu a garin Odigbo.

Sai dai Adegoroye ya ce har yanzu ba a gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar ba. Ya bayyana cewa ana jiran tawagar Ma’aikatar Lafiya ta jihar domin gudanar da gwaje-gwaje kan gawarwakin waɗanda suka mutu.

An dakatar da sayar da giya da aka sarrafa a gida

Adegoroye ya ce ƙaramar hukumar ta dakatar da sayarwa da shan giya da ake sarrafawa a gida a yankunan da abin ya shafa har sai an kammala bincike.

Ya ce wani binciken farko da aka yi ta hanyar tambayoyi da duba alamomin mutuwar ya nuna yiwuwar alaƙa tsakanin mutuwar da shan abubuwan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi barna da suka farmaki gidan shugaban jam'iyyar ADC

Sai dai ya jaddada cewa ana buƙatar ƙarin binciken lafiya domin tabbatar da hakan, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Gwamnatin Ondo ta fara bincike

Kwamishinan Lafiya na jihar Ondo, Banji Ajaka, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce gwamnatin jihar ta fara bincike domin gano abin da ya haddasa mutuwar mutanen.

Sai dai kwamishinan bai bayyana takamaiman nau’in abin da ake zargin mutanen suka sha ba.

’Yan sanda sun fara bincike

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Ondo, Abayomi Jimoh, ya ce rundunar ta fara cikakken bincike kan mutanen da suka mutu.

Ya ce ana zargin mutuwar na iya kasancewa da alaƙa da yiwuwar guba. Jimoh ya ce jami’an ’yan sanda, ciki har da ma’aikatan sashen kula da lafiyar ’yan sanda, suna aiki tare da Ma’aikatar Lafiya ta jihar da hukumomin lafiya na ƙaramar hukumar Odigbo.

A cewarsa, jami’an na tattara bayanai da hujjojin da za su taimaka wajen gano musabbabin mutuwar.

’Yan sanda sun gargadi jama’a

Jimoh ya yi kira ga jama’a da kada su yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba ko kuma su danganta mutuwar da wani takamaiman abu.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kai kazamin hari a Adamawa, an rasa rayukan bayin Allahl

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike da gwaje-gwajen dakin gwaje-gwaje.

Mutane 24 sun mutu a Ondo
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Mai maganin gargajiya ya yi damfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani makaho mai maganin gargajiya mai suna Owolabi Adefemi wanda aka fi sani da Ojunu ya damfari wata tsohuwa Naira miliyan 19.

Tsohuwar da aka damfara mai suna Madam Alimot ta kawo ‘yar ta ne wajen mai maganin gargajiyar don ya warkar da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng