Matashi Ya Aika Jami’in NDLEA Lahira bayan Caka Masa Wuka Mai Kaifi a Bauchi

Matashi Ya Aika Jami’in NDLEA Lahira bayan Caka Masa Wuka Mai Kaifi a Bauchi

  • Wani jami’in hukumar NDLEA ya rasa ransa bayan wani matashi ya caka masa wuka a cikinsa yayin gudanar da aikin hukuma a Bauchi
  • Lamarin ya faru a Anguwan Zango da ke Tilden Fulani, inda wasu matasa suka yi turjiya yayin da jami’an ke kokarin kama wani matashi
  • Hukumar NDLEA ta Bauchi ta ayyana wanda ake zargi da kisan jami’in a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Wani jami’in hukumar yaƙi da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA da ke jihar Bauchi ya rasa ransa bayan wani mutum da ba a san ko wanene ba ya caka masa wuka.

Rundunar NDLEA ta Bauchi ta ayyana wanda ake zargin da aikata kisan a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, yayin da ake kokarin gano sunansa da adireshinsa.

Kara karanta wannan

Kiran da Ahmad Gumi ya yi wa gwamnati bayan dambarwar matar Morocco

Ana neman matashi ruwa a jallo bayan kashe jami'in NDLEA
Taswirar jihar Bauchi da matashi ya kashe jami'in NDLEA. Hoto: Legit.
Source: Original

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin rundunar yan sanda a jihar Bauchi wanda ta wallafa a shafin Facebook.

Yadda aka caka wa jami'in NDLEA wuka

Rahotanni sun ce an caka jami’in wuka a cikinsa ne ranar Talata, yayin da yake gudanar da aiki tare da wasu jami’ai a Anguwan Zango.

Lamarin ya faru ne a Tilden Fulani, cikin ƙaramar hukumar Toro ta Bauchi, da misalin ƙarfe 11 na safe, kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida.

Mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce jami’an NDLEA sun isa yankin Zango ne domin dakile shaye-shayen miyagun kwayoyi tsakanin wasu matasa.

Ya ce jami’an sun kama ɗaya daga cikin matasan, sannan suka yi kokarin saka shi cikin motarsu domin tafiya da shi, amma wasu matasa suka yi turjiya.

Matashi ya caka wa jami'in NDLEA wuka
Kwamishinan yan sanda a Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, da matashin da ake nema ruwa a jallo. Hoto: Bauchi State Police Command.
Source: Facebook

Abin mazauna yankin ke cewa

Mazaunin yankin ya bayyana cewa, duk da cewa bai kasance a wurin ba, an sanar da shi cewa wani daga cikin matasan ya yi amfani da wani abu mai kaifi.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bindige babban manajan banki a Najeriya har ya mutu

Ya ce matashin ya caka wa jami’in NDLEA wuka ne yayin da yake kokarin hana kama wanda ake zargin da kuma taimaka masa ya kuɓuta.

Har ila yau, ya ƙara da cewa matasan sun gudu daga wurin bayan faruwar lamarin, inda suka bar jami’an NDLEA suna kula da abokin aikinsu da ya ji rauni.

Wani jami’in NDLEA da ke hedikwatar rundunar a Bauchi ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ƙi bayar da ƙarin bayani kan abin da ya faru.

Da aka tuntube shi ta WhatsApp domin tabbatar da rahoton, jami’in ya amsa da cewa:

“Eh, gaskiya ne.”

Dan sanda ya yi murabus kan rashin albashi

Mun ba ku labarin cewa rundunar ’yan sandan Bauchi ta fara bincike kan murabus ɗin wani ɗan sanda da ya ce bai samu damar cire albashinsa ba tsawon shekaru biyu.

Ta ce binciken farko ya nuna an riƙa biyan albashin jami’in akai-akai, amma matsalar BVN ce ta hana shi samun kuɗinsa.

’Yan sanda sun ce jami’in ya karya dokar amfani da kafafen sada zumunta bayan ya bayyana ƙorafinsa da murabus ɗinsa a intanet.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.