Wuta Ta Yi Wuta: An Kai Hare Hare Masu Zafi a Biranen Saudiyya
- Ƙungiyar Houthi ta kai hari kan biranen Khamis Mushait, Abha da Jizan na Saudi Arabiya da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa
- Hare-haren da aka kai a baya sun jikkata mutane 73 tare da haddasa gobara a wasu cibiyoyin samar da mai
- Ƙaruwar faɗa tsakanin Saudiyya da Houthi na ƙara fargabar sake komawa ga yaƙin da aka dakatar da shi tun bayan tsagaita wuta ta 2022
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Jeddah, Saudiyya - Rundunar hadin gwiwa da Saudiyya ke jagoranta da ke yaƙi da Houthi a Yemen ta ce mayakan ƙungiyar sun kai hari kan birane uku na Saudiyya.
Rundunar ta bayyana cewa mayakan Houthi sun kai hare-haren ne a biranen Khamis Mushait, Abha da Jizan da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa mai magana da yawun rundunar hadin gwiwar ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 9 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da yakin Iran, ƙasar Saudiyya ta kai munanan hare hare kan manyan birane 3
Ya ce mayakan Houthi na ci gaba da kai hare-haren da suka shafi kadarorin ƙasar da muhimman ababen more rayuwa na Saudiyya.
“Mayakan Houthi na ci gaba da kai munanan hare-hare kan kadarorin ƙasa da ababen more rayuwa na masarautar,” in ji sanarwar.
An yi gargadin yiwuwar haɗari
A safiyar ranar Laraba, Hukumar Kare Fararen Hula ta Saudiyya ta gargadi jama’a a lardin Khamis Mushait da birnin Abha kan yiwuwar fuskantar haɗari.
Daga baya hukumar ta ɗage wani gargaɗin da ta bayar a Khamis Mushait, kwana guda bayan hare-haren Houthi a birnin da wasu birane uku da ke kusa, cewar rahoton tashar Reuters.
Hare-haren sun jikkata mutane 73 tare da haddasa gobara a wasu cibiyoyin man fetur, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Mayakan Houthi sun kai hari Saudiyya
A ranar Talata, mayakan Houthi da ke samun goyon bayan Iran sun kai hari kan wani sansanin sojojin sama a Khamis Mushait da kuma wasu cibiyoyin samar da mai a biranen da ke kusa.

Kara karanta wannan
Dan takara ya yi alkawarin samar da lantarki a kowane gida cikin watanni 11 a Najeriya
An bayyana harin a matsayin ɗaya daga cikin manyan hare-haren da aka kai a Saudiyya tun bayan fara yaƙin da Amurka da Isra’ila suka yi wa Iran a watan Fabrairun 2026.
Mahukuntan Saudiyya ba su bayyana dalilin da ya sa aka bayar da sabon gargaɗin a Khamis Mushait ranar Laraba ba.
Tsoron sake komawa yaƙi
Yaƙin da ke tsakanin Saudiyya da mayakn Houthi ya ƙara tsananta a cikin watannin baya-bayan nan, lamarin da ya haifar da fargabar sake komawa wani yaƙi mai girma.
A shekarar 2022, tsagaita wuta da Majalisar Ɗinkin Duniya ta taimaka wajen cimmawa ta rage yaƙe-yaƙen da suka shafe shekaru ana yi a Yemen.
Saudiyya ce ke jagorantar wata rundunar hadin gwiwar ƙasashen Larabawa da ke goyon bayan gwamnatin Yemen mai hedikwata a kudancin ƙasar.
Gwamnatin ta bar babban birnin Yemen, Sanaa, bayan da mayakan Houthi suka ƙwace birnin daga hannunta shekaru 12 da suka gabata.

Source: Getty Images
Saudiya ta kai hare-hare a Yemen
A wani labarin kuma, kun ji cewa jiragen yakin Saudiya na kai hare-haren sama a wasu larduna daban-daban na kasar Yemen.
Hare-haren sun shafi lardunan Marib, al-Jawf da Taiz, inda aka ruwaito cewa Saudiyya ta yi luguden wuta a yankin Khab wa Sha'af da ke lardin al-Jawf.
Asali: Legit.ng