Kashim Ya Fada wa Abokai da Masoya Abin da Yake Bukata wajensu da Ya Cika 60

Kashim Ya Fada wa Abokai da Masoya Abin da Yake Bukata wajensu da Ya Cika 60

  • Kashim Shettima ya ce cikarsa shekaru 60 lokaci ne na yin tunani da mika godiya ga Allah maimakon a yi ta shagali
  • Ya roki magoya bayansa da kar su yi tallar taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa ko a yi bikin cikarsa shekaru 60
  • Mataimakin shugaban kasar ya yi kira da a maida hankali wajen yi wa Najeriya addu'o'in samun nasara da kuma ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya cika shekara 60 a duniya, kuma za a samu masu taya shi murna.

To sai dai, Kashim Shettima ya nuna bai bukatar masoya da abokan arziki su kashe kudi su shirya biki saboda ya kara shekara.

Kashim Shettima
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima yana sauko wa daga jirgi a Abuja Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Kashim Shettima bai so a shirya masa biki

A maimakon a yi facaka da dukiya, Kashim Shettima ya yi rubutu a Facebook ranar Talata yana cewa bai bukatar duk wadannan.

Kara karanta wannan

EFCC ta gano bakuwar dabarar da ma’aikata suke bi su sace kudin gwamnati

Mataimakin shugaban Najeriyan ya nemi magoya baya, abokan siyasa da aminai su karkatar da kudin zuwa sadaka da makamantansu.

Kamar yadda ya saba yi, a bana ma ya roki masoyansa su yi abubuwa masu amfani a madadin a yi ta aiko masa da kyaututtuka.

Ma'anar shekaru 60 wajen Kashim Shettima

Premium Times ta rahoto shi ya ce a wannan gaba da ya kai a rayuwa, ya kamata ne a ya zama abin koyi kuma ya kasance mai godiya.

"60 shekaru ne da mutanenmu suke sa ran mutum ya rabu da gigin sha’awa, ya koma nazari mai zurfi, ya musanya gadara da godiya, ya daina mayar da hankali kan tara abin duniya, ya fahimci hikimar sakin hannu.
Saboda haka ina sake kira ga duk mai yi mani fatan alheri da ka da ya kashe kudi domin murnar ranar nan, sai dai ya yi amfani da duk wata dukiya da suka yi niyya a wajen sadaka, ko ga mutanen da duk suka ga dama a ko ina a kasar mu."

Kara karanta wannan

Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba

- Kashim Shettima

Sanata Shettima ya ce irin wannan taimako duk kankantarsa, zai yi tasiri a rayuwar bayin Allah.

Jawabin tsohon gwamnan ya kara da cewa darajar al’umma tana karuwa ne da irin kulawa da taimakon da take ba marasa hali.

Ya ce irin wannan taimako ba ya kadan sannan ba ya yawa saboda yanayin samun kowa.

Kashim ya ce a sa Najeriya a addu'a

Kashim Shettima ya cigaba da neman a yi wa kasa addu'a:

"A wuri na, wannan yana cikin mafi kyawun addu’ar da mutum zai iya yi a madadi na."
Kashim Shettima
Kashim Shettima da ya isa taron AU zai wakilci Najeriya Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Maimakon talla a jaridu da bukukuwa da rabon kyaututtuka saboda murnar ya kai shekaru 60, ya nemi a yi wa Najeriya addu’a.

Ya kare da bayanin baiwar da Ubangiji ya yi wa kasar nan na matasa da mutane kabilu dabam-dabam masu son neman kan su.

An gargadi lauyoyi a shari'ar Tinubu-Atiku

Kun ji labari an gargadi lauyoyi su kauce wa tattauna batun shari’ar Atiku Abubakar da Bola Tinubu a kafafen yada labarai ko shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

Tinubu zai cigaba da aiki daga turai, babu zancen mika wa Kashim ragamar mulki

Alkalin kotun tarayya, Mai Shari’a Inyang Ekwo zai hukunta duk wani lauya da aka samu yana ta sakin bakin shi game da wannan shari'a da ake yi a kotu.

Ana so a gujewa hakan ne duba da yanayin shari'ar, tunda ta shafi Bola Tinubu da takarar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng