Ado Gwanja Ya Yi Magana ana Cewa Yana Fama da Rashin Lafiya Mai Tsanani

Ado Gwanja Ya Yi Magana ana Cewa Yana Fama da Rashin Lafiya Mai Tsanani

  • Datti Assalafy ya yi magana kan fitaccen mawakin Kannywood, Ado Gwanja, inda ya ce yana fama da rashin lafiya da ya kwashe sama da kwanaki 40
  • Malamin ya ce jinyar ta zama babban darasi ga Gwanja da sauran masu rayuwa irin tasa, yana mai jan hankalinsu su koma ga Allah
  • Sai dai Ado Gwanja ya mayar da martani , inda ya ce wasu mutane suna mayar da rayuwarsa abin da suka damu da shi duk da cewa bai yi musu komai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano– Mai amfani da kafar sada zumunta, Datti Assalafy, ya yi magana game da mawakin Kannywood Ado Gwanja a lokacin da ake cewa yana fama da rashin lafiya.

Datti ya bayyana jinyar mawakin a matsayin babban darasi a rayuwa, inda ya yi kira gare shi da sauran masu bibiyar irin rayuwarsa da su yi tunani kan makomarsu.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi magana mai tsauri kan kisan fitaccen mai sharhi kan siyasa a Kano

Mawakin Najeriya, Ado Gwanja
Mawakin Hausa, Ado Gwanja. Hoto: Ado Gwanja
Source: Facebook

A cikin wani rubutu da ya wallafa a Facebook, Datti ya bayyana Ado Gwanja a matsayin mawaki kuma ɗan wasan fina-finan Hausa daga Kannywood.

Abin da Datti ya ce kan Gwanja

Datti ya yi zargin cewa wasu daga cikin wakokin Ado Gwanja da kuma yadda yake bayyana a fina-finai sun kasance suna ƙarfafa wasu dabi'u da ya bayyana a matsayin sun saɓa wa tarbiyyar Musulmi.

Ya kuma ambaci wani lauya, Badamasi Gandu, wanda ya taɓa shigar da ƙara kan Ado Gwanja saboda abubuwan da ya ce suna cikin wakokinsa.

Datti ya kuma yi magana kan wani umarnin wata babbar kotun Shari'ar Musulunci da ke Kano a shekarar 2024, wanda ya shafi kama Ado Gwanja domin gudanar da bincike kan zargin abubuwan da ake dangantawa da wakokinsa.

Ya ce a halin yanzu Gwanja yana fama da jinya mai tsanani, inda ya yi ikirarin cewa mawakin ya kwashe sama da kwana 40 yana jinya kuma ba ya iya tashi da kansa.

Kara karanta wannan

Pantami ya ce ba ya fargabar cin zaben 2027, ya fadi irin mulkin da zai yi a Gombe

Datti ya ce ya ga wasu bidiyoyi na abokan Gwanja suna magana kan halin da yake ciki, inda wasu suka yi zargin cewa matsalar na da alaka da sihiri.

Martanin Ado Gwanja

A nasa martanin, Ado Gwanja ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Facebook, inda ya ce abin mamaki a rayuwa shi ne yadda mutum zai iya barin kowa ya yi rayuwarsa cikin kwanciyar hankali, amma wasu su mayar da rayuwarsa abin damuwarsu.

A wani sako da ya wallafa a Facebook, Gwanja ya ce wasu mutane idan suka kasa samun wani laifi na gaskiya da za su jingina wa mutum, sai su koma hayaniya.

Ado Gwanja
Lokacin da Ado Gwanja ke waka. Hoto: Ado Gwanja
Source: Facebook

Ya kammala saƙonsa da cewa yana gode wa Allah, inda ya rubuta:

“Alhamdulillah.”

Jaruma Zee Diomond ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitacciyar jarumar Kannywood, Zainab Diamond, wadda aka fi sani da Maman Bintalo a shirin Labarina, ta rasu.

An ruwaito cewa jarumar ta rasu ne bayan Sallar Asuba, bayan ta shafe wani lokaci tana karɓar magani. Rasuwarta ta jefa abokan aiki da masoyanta cikin alhini.

Mutane da dama sun yi mata addu'o'i domin suna rokon Allah ya gafarta mata ya kuma sanya jinyar da ta yi ta zamo kaffara a gare ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng