Ana Wata ga Wata: Daukar Kirista a Matsayin Mataimakin Gwamna Ya Tada Kura a Arewa

Ana Wata ga Wata: Daukar Kirista a Matsayin Mataimakin Gwamna Ya Tada Kura a Arewa

  • Zaɓin Jerry Adams, Kirista daga Kudancin Kaduna, da Gwamna Uba Sani ya yi a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2027 ya sake buɗe muhawara
  • Matakin ya dawo da tsarin tikitin Musulmi da Kirista da ya fi rinjaye a siyasar Kaduna tun bayan komawar mulkin dimokuraɗiyya a 1999
  • Sai dai wasu Musulmai a Arewacin Kaduna na ganin ya kamata jam’iyyar APC ta ci gaba da tsarin tikitin Musulmi da Musulmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Matakin gwamnan Kaduna, Uba Sani na daukar Jerry Adams, wani Kirista daga Kudancin Kaduna, a matsayin abokin takararsa a zaɓen gwamna na 2027 ya bude sabon babin muhawarar siyasa mai zafi.

Matakin ya dawo da tsarin tikitin Musulmi da Kirista da ya fi shahara a siyasar Kaduna tun bayan komawar mulkin dimokuraɗiyya a 1999.

Kara karanta wannan

Kiristan da ya yi aiki da El Rufa'i ya fadi me ya faru a Kudancin Kaduna

Uba sani.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani a fadar gwamnatinsa Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

El-Rufai ya ɓullo da musulim-muslim

Haka kuma, Daily Trust ta ce ya sauya tsarin tikitin masu addini ɗaya da tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya bullo da shi bayan rasuwar mataimakinsa, Barnabas Bala, wanda aka fi sani da Bantex.

El-Rufai ya zaɓi Hadiza Balarabe, Musulma daga Ƙaramar Hukumar Sanga da ke Kudancin Kaduna, a matsayin abokin takararsa, inda ya kare matakin a matsayin dabarar siyasa.

Tsarin ya ci gaba lokacin da Uba Sani ya zama gwamna a 2023, inda Hadiza ta zama abokiyar takararsa sannan daga bisani mataimakiyar gwamna.

Uba Sani ya dauki kirista a 2027

Amma yayin da wa’adinta na biyu da kundin tsarin mulki ya kayyade ke gab da ƙarewa, uba Sani ya koma tsohon tsarin inda ya zaɓi Adams, ɗan ƙabilar Moroa (Marwa) daga Ƙaramar Hukumar Kaura ta jihar.

A fannin siyasa, matakin ya bayyana cewa ya ƙarfafa damar APC na samun ƙarin karɓuwa a Kudancin Kaduna, yankin da a al’adance ake danganta shi da jam’iyyun adawa.

Kara karanta wannan

'Minista ya fi ka gaskiya': An bukaci El Rufai ya ba Kudancin Kaduna hakuri

Babban ƙalubalen da APC ke fuskanta yanzu shi ne ko sabon tsarin tikitin zai iya sauya lissafin siyasa a yankin.

An fara magana kan daukar Kirista

Wani mazaunin Sabon Garin Tudun Wada, Bello Idris, ya ce mai yiwuwa gwamnan ya yi kuskure wajen watsi da tsarin tikitin masu addini ɗaya.

“Matakin zai shafi ƙuri’un gwamnan, musamman a arewacin Kaduna da suka goyi bayan tsarin tikitin masulmi da musulmi.
"Dabarar ce aka yi amfani da ita wajen lashe zaɓen da ya gabata, amma gwamnan ya sauya ta ne saboda yana son ƙarin ƙuri’u daga Kuancin Kaduna,” in ji shi.

Tasirin ƙabilu a Kudancin Kaduna

Ko da yake Adams ɗan Kudancin Kaduna ne, wasu mazauna yankin na ganin bai fito daga cikin manyan kabilun masu zaɓe na yankin ba. Al’ummar Moroa da yake wakilta a Kaura ba ta da yawan jama’a kamar Bajju, Atyap, Ikulu da Kamanton.

Wani mazaunin Kudancin Kaduna, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce zai yi wuya Adams ya samu cikakken goyon bayan mutanen Bajju, saboda Irmiya Kantiok, abokin takarar Isa Ashiru Kudan, ɗan takarar ADC na kujerar gwamna, shi ma ɗan ƙabilar Bajju ne.

Kara karanta wannan

Gawuna ya yi matsaya tsakanin shiga APC da zama a NDC tare da Kwankwaso

“Ba za ka ce min mutanen Bajju za su yi watsi da ɗansu su zaɓi wani mutum ba saboda kawai dukansu daga yanki ɗaya suke,” in ji shi.

Sai dai shugaban kungiya yan jaridan Kudancin Kaduna, Ango Bally, ya yi watsi da hujjar cewa ya kamata a dogara da yawan jama’a kaɗai wajen samun goyon bayan siyasa a yankin.

Uba Sani.
Gwamnan Uba Sani tare da sabon abokin takararsa a zaben 2027, Jerry Adams Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

Ya ce mutanen Zangon Kataf, wanda ake kallonsa a matsayin hedkwatar siyasa ta Kudancin Kaduna, sun yi imani da adalci da daidaito.

Ya ce Adams na da tasirin siyasa da karɓuwa a tsakanin mutane masu shekaru daban-daban a Kudancin Kaduna, duk da cewa Kantiok shi ma ɗan yankin ne.

Ana zargin El-Rufai ya raba Kaduna

Kun ji cewa Ministan tsaro, Christopher Musa, ya zargi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, da aikata abubuwa marasa kyau da suka haifar da rarrabuwa kai a jihar.

Ya yi zargin cewa El-Rufa'i ya raba jihar gida biyu ta hanyar manufofinsa, wanda hakan ya sa mutane ba sa iya zama da juna a Kudanci da Arewacin Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262