Zaben 2027: Rokon da Bola Tinubu Ya Yi ga Malaman Addini a Najeriya

Zaben 2027: Rokon da Bola Tinubu Ya Yi ga Malaman Addini a Najeriya

  • Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bukaci shugabannin Kirista su yi amfani da mimbari wajen yaɗa zaman lafiya
  • Tinubu ya ce shugabannin addini su yi kira ga jama’a su guji sayen ƙuri’a, kalaman ƙiyayya da amfani da ƙabila ko addini
  • Kungiyar shugabannin Kirista ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu a zaben 2027, tana cewa za ta ci gaba da mara masa baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gabanin babban zaben 2027, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya shawarci malaman addinin Kirista a Najeriya.

Tinubu ya bukaci shugabannin Kirista su inganta zaman lafiya da shiga zaɓe cikin mutunci ba tare da cin zarafi ba.

Tinubu ya shawarci fastoci a Najeriya kan siyasa
Shugaba Bola Tinubu yana duba takardu a ofishinsa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Tinubu ya shawarci malaman addini

Tinubu ya yi wannan kira ne ranar Laraba a Abuja, yayin taron 2026 na ƙungiyar 'International Synod of Charismatic Archbishops', cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kungiyar APC ta yi barazanar fallasa sanata Ali Modu Sheriff

Shugaban ƙasar, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya wakilta, ya ce Cocin na da muhimmiyar rawa wajen haɗa kan jama’a.

Ya ce ya kamata shugabannin Kirista su taimaka wajen rage rarrabuwar addini da ƙungiyoyi, tare da tabbatar da cewa siyasa ba ta haddasa tashin hankali.

Tinubu ya ce:

“A matsayinku na fastoci masu kishin addini, kuna da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa Najeriya ba ta yi asara ba.
“Ina roƙonku ku ƙarfafa mutane su shiga zaɓe cikin zaman lafiya da fahimtar juna, tare da guje wa duk wani abu da zai kawo rikici.”

Ya bukaci shugabannin su yi magana kan munanan ayyukan zaɓe, ciki har da sayen ƙuri’a, kalaman ƙiyayya da amfani da ƙabila ko addini wajen rura rikici.

Tinubu ya kuma bukaci a gudanar da kamfen bisa muhimman batutuwa, yana mai cewa bai kamata burin ’yan siyasa ya zarce zaman lafiya da muradun ƙasa ba.

Shugaban ƙasar ya kuma yi gargadin kada a mayar da mimbari wajen tunzura jama’a, maimakon amfani da shi wajen gina kyakkyawan tunani da lamiri.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ware gwamna a Arewa ya kwararo masa yabo

Ya ce:

“Wannan kira ba zai cika ba idan ban gargaɗe ku da ku guji mayar da mimbari kayan tunzura jama’a ba, maimakon wurin tarbiyyar lamiri.”
Tinubu ya nuna damuwa kan siyasar gaba da kabilanci
Shugaba Bola Tinubu da ke neman tazarce karkashin APC. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Shawarar ministan yada labarai ga al'umma

A nasa ɓangaren, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bukaci shugabannin addini su taimaka wajen hana matasa shiga tsattsauran ra’ayi da aikata laifuka.

Idris ya ce shugabannin addini su tallafa wa tsarin gano alamun rikici tun da wuri a al’umma, tare da amfani da tattaunawa wajen magance matsaloli.

Ministan ya sake tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta kare ’yancin addini, domin Kiristoci, Musulmai da sauran masu bin addinai su rayu cikin zaman lafiya.

Ya ce:

“Kada a bari wani zaɓe ya sa Kirista ya zama maƙiyin Musulmi, Musulmi ya zama maƙiyin Kirista, Arewa ta zama maƙiyin Kudu, ko ƙabila ta zama maƙiyin wata.”

Oluremi ta roki yan Najeriya kan Tinubu

An ji cewa Uwargidan shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta roƙi ’yan Kudu maso Gabas su sake zaɓar mijinta, Bola Tinubu, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

Duk da shirin haɗakar yan adawa, Jigon PDP ya sallama wa Shugaba Tinubu a zaben 2027

Oluremi Tinubu ta ce tana son ganin Najeriya ta inganta kafin ta tsufa, yayin da ta bayyana cewa ita da shugaban ƙasa suna aiki don cigaban ƙasar.

Uwargidan shugaban ƙasar ta ƙarfafa mata 2,500 a Imo da kayan sana’a, sannan ta sanar da ƙarin tallafin N100,000 ga mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.