An Shirya Samar da Kotu, Gwamna Zai Kama Yara a Titi da ba Su Zuwa Makaranta
- Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya ce za a kama duk yaran da suka isa makaranta da aka samu kan tituna lokacin karatu
- Gwamnatin Nasarawa ta tanadi littattafai, kayan makaranta, safa da jakunkuna domin rabawa yaran da aka dawo da su makaranta
- Gwamnatin jihar ta kuma amince da daukar sabbin malamai 1,000 tare da sakin N2bn domin biyan fansho da alawus na ma’aikatan da suka yi ritaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa - Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana aniyar gwamnatinsa na tabbatar da inganta ilimi a fadin jihar.
Gwamna Sule ya bayyana cewa gwamnatin jiharsa ta shirya kama duk yaran da suka isa makaranta da aka samu kan tituna lokacin karatu.

Source: Facebook
Sule ya bayyana hakan ne ranar Laraba ta bakin babban mataimakinsa na harkokin jama’a, Peter Ahemba, yayin taron manema labarai na wata-wata a Lafia, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan
Pantami ya ce ba ya fargabar cin zaben 2027, ya fadi irin mulkin da zai yi a Gombe
Shirin gwamnatin Nasarawa game da ilimi
Gwamnatin ta kuma ce tana duba yiwuwar kafa kotunan tafi-da-gidanka domin gurfanar da iyayen yaran da aka samu suna yawo a kan tituna a lokacin da ya kamata su kasance a makaranta.
Ya ce matsalar yaran da ba su samu horo da kuma wadanda ba sa zuwa makaranta na haifar da babban hadari ga makomar jihar.
Gwamnan ya ce hukumar ilimin bai daya ta jihar ta tanadi littattafai, kayan makaranta, safa da jakunkuna da yawa domin rabawa yaran da aka samu kan tituna.
Ya ce za a mayar da yaran makarantu domin su ci gaba da karatu, tare da tabbatar da cewa sun samu damar cin moriyar ilimi.
Ya ce:
“Saboda a karshen wannan rangadin wayar da kan jama’a da Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jiha za ta gudanar domin tabbatar da cewa yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta da ba sa zuwa makaranta sun koma, bayan wa’adin sassaucin wayar da kan jama’a, gwamnati za ta fara cikakken aiwatar da dokar. “Za a kafa rundunar aiki da za a dora wa alhakin zagayawa kan tituna. Idan aka gano irin waɗannan yara a lokacin makaranta, za a tsare su domin gano iyayensu.”

Source: Original
Sauye-sauye da aka kawo bangaren ilimi
Dokar ta tanadi cewa ilimin firamare kyauta ne kuma dole ne duk yaran da suka kai shekarar zuwa makaranta su samu damar karatu, cewar Punch.
Gwamnan ya kuma ce ya amince da shugaban hukumar ilimin bai daya ya bayar da takardun daukar aiki ga sabbin malaman firamare 1,000.
Ya ce daukar malaman zai taimaka wajen rage matsalar karancin malamai a makarantun firamare kafin a koma makarantu domin sabon zangon karatu.
Sule ya kara bayyana cewa gwamnatin jihar ta saki N2bn domin biyan kudaden fansho da alawus ga ma’aikatan da suka yi ritaya daga shekarar 2013 zuwa yanzu.
Buri na bayan na kammala mulki- Gwamna Sule
A baya, an ji cewa Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce burinsa shi ne a tuna da shi a matsayin wanda ya fitar da jihar daga mawuyacin hali.
Sule ya ce gwamnatinsa ta inganta hadin kan al’umma, rage tasirin jam’iyyun adawa, tare da kara bunkasa masana’antu.
Gwamnan ya bayyana Nasarawa a matsayin “lu’u-lu’u da ke boye”, yana mai cewa gwamnatinsa ta bude damarmakin jihar.
Asali: Legit.ng
