'Yan Sanda Sun Bi Masu Garkuwa har cikin Daji Sun Masu Jina Jina

'Yan Sanda Sun Bi Masu Garkuwa har cikin Daji Sun Masu Jina Jina

  • Rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta gudanar da wani samame a ƙaramar hukumar Ikara, inda ta kubutar da mutane biyu da aka yi garkuwa da su
  • Jami’an tsaro sun kuma tarwatsa sansanin masu garkuwa da mutane tare da kashe biyu daga cikin waɗanda ake zargi da aikata laifin
  • Sai dai jami’an ’yan sa-kai uku sun rasa rayukansu yayin samamen, yayin da wasu ’yan sanda biyu suka samu raunukan harbin bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta gudanar da wani samame a ranar Talata, 8 ga Satumba 2026, inda ta kai farmaki kan wuraren da ake zargin masu garkuwa da mutane ke fakewa a ƙaramar hukumar Ikara.

Jami’an rundunar, ƙarƙashin jagorancin jami’in ‘yan sanda na Ikara, sun gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron sa-kai da kuma Rundunar Hadin Gwiwar Fararen Hula, CJTF.

Kara karanta wannan

Ana zargin Bello Turji da kai mummunan hari a Sokoto da aka sace mutane 40

Yan sanda a dajin Kaduna
Dajin Ikara da 'yan sanda suka shiga suka kai farmaki. Hoto: Masur Hassan
Source: Facebook

Kakakin 'yan sanda ya wallafa a Facebook cewa sun samu sahihin bayani kan kasancewar wasu da ake zargi da garkuwa da mutane a yankunan Auchanawa da Wambai na ƙaramar hukumar Ikara.

An tarwatsa masu garkuwa

Bayan jami’an tsaron sun isa wurin da aka gano, an yi musayar wuta tsakaninsu da waɗanda ake zargin ’yan ta’addan ne.

Rundunar ta ce jami’anta sun yi nasarar share dazuzzukan da ke yankin tare da tarwatsa sansanin masu garkuwa da mutanen.

A yayin samamen ne aka kubutar da mutane biyu da aka yi garkuwa da su, inda rundunar ta ce an same su cikin ƙoshin lafiya.

An kashe masu garkuwa biyu

Rundunar ’yan sandan ta ce an kashe wasu mutane biyu da ake zargi da kasancewa cikin masu garkuwa a yayin musayar wutar.

Ta ƙara da cewa wasu daga cikin 'yan ta'addan sun tsere zuwa cikin dazuzzukan da ke kewaye, wasu daga cikinsu kuma na iya kasancewa sun samu raunukan harbin bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bindige babban manajan banki a Najeriya har ya mutu

Sai dai samamen ya zo da asarar rayuka, inda mambobin CJTF guda uku suka rasa rayukansu.

’Yan sanda 2 sun samu raunuka

Rundunar ta ce wasu jami’an ’yan sanda biyu sun samu raunukan harbin bindiga a yayin artabun. A halin yanzu, jami’an biyu na samun kulawar likitoci domin duba lafiyarsu.

Kwamishinan ’yan sandan Kaduna, CP Muhammad Rabiu, ya jajanta wa iyalan mambobin CJTF da suka rasa rayukansu tare da yi wa jami’an ’yan sandan da suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Rundunar ta buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa ’yan sanda sahihan bayanan sirri cikin lokaci domin taimakawa wajen gano wuraren da masu aikata laifi ke fakewa.

An kashe manajan banki

A wani labarin, mun ruwaito cewa Bankin Polaris ya bayyana alhininsa kan kisan wani manajan reshensa da aka bayyana da suna Mista Ossy, a Imo.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 6 ga Satumba 2026, a harabar jami’ar FUTO, lokacin da ma’aikacin bankin, wanda ke aiki a Owerri, yake kai yaransa makaranta.

Rahotanni sun bayyana cewa bankin ya ce yaran sun samu damar tserewa daga wurin, amma ma’aikacin nasa ya rasa ransa yayin harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng