Kiran da Ahmad Gumi Ya Yi wa Gwamnati bayan Dambarwar Matar Morocco
- Ahmad Gumi ya nemi gwamna ya sa baki domin kotun shari’a ta warware auren wata 'yar Morocco da ke fuskantar cin zarafi
- Malamin ya ce bai kamata mace da ke neman kubuta daga aure mai cutarwa ta biya mijinta kudi ko ta rasa hakkokinta a kotu ba
- Gumi ya buƙaci a yi gyara a kotuna ta yadda za su saurari batutuwan auratayya cikin sauri, adalci da tausayi a jihar Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi kira da a gaggauta gyara dokokin shari’ar Musulunci na aure a jihar Kaduna.
Babban malamin addinin ya yi wannan kira ne bayan an dauki lokacin ana ta zarginsa da boye matar wani ‘dan kasuwa a gidansa.

Source: Facebook
Ahmad Gumi yana rokon a raba aure a kotu
Yanzu da matar ta yi wa duniya jawabi a Facebook, Ahmad Abubakar Gumi ya bukaci a yi amfani da lamarin wajen ganin an kawo gyara.
Da farko malamin ya roki gwamnatin Uba Sani ta yi amfani da kotun shari’a wajen gaggawar raba auren Khadija Diab da Nasir Idris Musa.
Ya ce Khadija Diab ta ci wahala a zaman auren da ta yi da wannan mutumi, kuma bai kamata a bari ta cigaba da shan wata azaba a kotu ba.
Abin da ya roka shi ne bangaren shari’a ya saukake mata, ya kawo karshen bakin lamarin.
Baya ga haka, Sheikh Ahmad Gumi yana so shari’a ta tursasa wa Nasir Idris ya biya Diab bashin duk wasu kudi da aka ce tana bin shi.
‘Dan kasuwa ya karbi aron kudinta bai biya kamar yadda malamin ya rubuta a kafar Facebook.
Duk da matar ce ta nemi saki ta hanyar khul’i, Ahmad Gumi ya ce bai kamata a ce sai ta biya wasu kudi za ta fanshi kanta daga mutumin ba.

Kara karanta wannan
Ministan tsaro ya sa Majalisar kolin harkokin Musulunci ta dauki zafi a shari’ar El Rufai
Gumi ya yi kira a gyara kotunan shari'a
Don haka ya bukaci a yi amfani da wannan dama wajen kawo gyara a kotunan shari’a ta yadda za su yi aiki kan lokaci yadda ya kamata
"Dole a yi wa tsarin shari’armu garambawul saboda ya yi aiki da kyau kuma a yi gaggawar tabbatar da adalci.
"Zargin rashin gaskiya da tara tulin shari’u, tsauraran sharudan karbar hujja da bata-lokaci babu gaira babu dalili bai kamata su maida neman adalci ya zama hanyar karin wahala ba."
- Ahmad Gumi
Malamin ya ce idan shari’o’in da suka shafi mata za su yi shekara da shekaru a kotu, to an yi barna a gidaje da dangogin bayin Allah.
Abin da ake so gwamnatin Kaduna ta yi
Masanin fikihun ya nuna bai jin dadin yadda ake rike mata da igiyar auren da babu dadi.
A kiran da ya yi wa Uba Sani, ya bukaci kotuna su maida hankali wajen harkar sakin khul’i da kuma batun rike yara bayan saki.
Ya kuma kawo zancen cin zarafi da sauran rigingimun gidan aure, yana so gwamnatin Kaduna ta kawo sauyi a kotunan musulunci.
Lauya ta ce Khadijah Diab tana Morocco
Lauyar Khadija Diab, ta musanta zargin cewa Sheikh Ahmad Gumi yana rike da ita, ta ce matar tana kasarta ta Morocco tun watan Afrilu 2026.
Wata kungiyar kiyaye hakkin mata ta taimaka mata samun takardar tafiya don komawa gida bayan zargin mijinta da rike mata fasfo da kuma cin zarafi.
An shigar da sabuwar kara a kotun Shari'a a watan Yulin 2026 don neman raba auren Khadija da mijinta, Nasiru Idris Musa, bisa tafarkin Musulunci.
Asali: Legit.ng

