Ana Shirin Zaben 2027, Gwamna Abba Ya Aika Sako ga 'Kwankwaso' da 'Yan Siyasa a Kano
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargadi yan siyasa,agoya baya da jam'iyyu yayin da ake shirye-shiryen zaben 2027
- Abba ya bukaci jam’iyyun siyasa da magoya bayansu kan gujewa kalaman kiyayya, tsokana, barazana da tashin hankali yayin da yakin neman zabe
- Ya bukaci ‘yan takara su mayar da hankali kan manufofi, tsare-tsare da ayyukan da suka yi, maimakon zagi da bata suna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargadi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu kan kalaman kiyayya, tsokana, barazana da tashin hankali.
Gwamna Abba ya yi wannan gargadi ne ga dukkan yan siyasar Kano yayin da aka fara yakin neman zaben gwamna na 2027 a hukumance.

Source: Facebook
Abba ya ja kunnen yan siyasar Kano
Ya yi wannan gargadin ne ta hannun daraktan yada labarai da wayar da kan jama’a na gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a wani taron manema labarai da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Gwamnan ya bukaci ‘yan takara da magoya bayansu su mayar da yakin neman zaben kan batutuwan da suka shafi jama’a, yana mai cewa ya kamata siyasa ta kasance kan manufofi, tsare-tsare, tarihin ayyuka da shirye-shirye, ba zagi da bata suna ba.
“Mu yi takara bisa ra’ayoyi, manufofi, tarihin ayyuka da shirye-shirye, maimakon zagi, barazana ko tashin hankali," in ji shi.
An gargadi masu tada zaune tsaye
Abba Kabir Yusuf ya kuma yi gargadi kan lalata dukiyoyi da duk wani mataki da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar da ake samu a jihar Kano.
Ya bukaci magoya bayansa su kasance masu da’a, su mutunta ra’ayoyin abokan hamayya, sannan su guji fadawa tarkon tsokana da za ta iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a.
Haka zalika, gwamnan ya bukaci masu amfani da kafafen yada labarai, masu rubutun ra’ayi a shafukan intanet, ‘yan jarida da masu amfani da kafafen sada zumunta su rika tantance bayanai kafin wallafa su.
Ya gargade su da gujewa yada labaran karya, jita-jita, abubuwan da ke tunzura jama’a da bayanan da ba su da inganci.
Gwamna ya yi magana kan jami’an tsaro
Gwamnan ya bukaci jami’an tsaro su kasance masu kwarewa, adalci da sanya ido a duk lokacin yakin neman zaben.
Ya kuma bukaci jam’iyyun siyasa da kungiyoyin yakin neman zabe su hada kai da jami’an tsaro tare da bin dukkan ka’idojin da doka ta tanada.

Source: UGC
Abba ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da ayyuka da gudanar da shirye-shiryen ci gaba ba tare da la’akari da lokacin siyasa ba.
Ya ce Kano ta fi kowace jam’iyyar siyasa ko mutum girma, yana mai jaddada cewa bayan kammala zabe, ‘yan siyasa za su ci gaba da zaman tare da juna.
Wani dan Kano, Aminu Sulaiman ya goyi bayan kiran da gwamna ya yi yayin da yake bayyana wa wakilin Legit Hausa ra'ayinsa gabanin zaben 2027.
Aminu ya ce Kano ta yi kaurin suna wajen ayyukan dabar siyasa da sanya kiyayya tsakanin magoya bayan yan siyasa, yana mai cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen haka.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya yi magana mai tsauri kan kisan fitaccen mai sharhi kan siyasa a Kano
Matashin ya bukaci yan uwansa Kanawa su daina fadawa tarkon yan siyasa, kuma kada su bari banbancin ra'ayin siyasa ya sa su gaba ko fada da yan uwansu.
Gwamna Abba ya raba tallafi ga mata
Kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da fara rabon tallafin Naira miliyan 290 ga mata 5,800 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Gwamna Abba ya bayyana cewa an gayyaci kashi 20 cikin 100 na wadanda suka amfana daga kowace karamar hukuma domin halartar bikin kaddamar da shirin.
Ya ce kowace daga cikin matan da za su amfana da shirin za ta samu N50,000 domin fara sabuwar sana'a ko fadada wadda take yi.
Asali: Legit.ng

