Shettima Ya Kwatanta Farin Jinin Buhari da Peter Obi, Ya Fadi Wanda Ya Yi Zarra
- Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi iƙirarin cewa Peter Obi ba shi da farin jinin da marigayi Muhammadu Buhari ya samu a Najeriya
- Shettima ya yi wannan furuci ne a Anambra yayin gangamin APC na neman wa’adin mulki na biyu ga Shugaba Bola Tinubu, tare da Gwamna Chukwuma Soludo
- Ya bukaci al’ummar Kudu maso Gabas su ƙarfafa alaƙa da sauran yankunan Najeriya, yana mai cewa samun goyon baya daga sassa daban-daban na ƙasa na da muhimmanci wajen lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Anambra - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ba zai kai farin jinin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba.
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamban 2026 a jihar Anambra, yayin da yake jagorantar gangamin yaƙin neman zaɓe domin neman wa’adin mulki na biyu ga Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Shettima ya kwantar da hankalin 'yan Igbo, ya yi masu albishir kan kujerar shugaban kasa

Source: Facebook
Gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo, ya halarci gangamin tare da mataimakin shugaban ƙasar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Shettima ya ce ƙoƙarin da Buhari ya sha yi na neman shugabancin Najeriya kafin nasarar da ya samu a shekarar 2015 ya nuna muhimmancin gina ƙaƙƙarfan goyon baya a faɗin ƙasar.
Ya ce Igbo na da muhimmanci a Najeriya
Mataimakin shugaban ƙasar ya bukaci al’ummar Kudu maso Gabas da kada su ɗauka cewa ana mayar da su saniyar ware a tsarin siyasar Najeriya.
Ya jaddada cewa al’ummar Igbo na da muhimmiyar rawa a harkokin siyasa da tattalin arzikin ƙasar.
Shettima ya ce akwai kusan ’yan Igbo miliyan 17 da ke zaune a Arewacin Najeriya, yayin da wasu miliyan 10 ke zaune a Legas kaɗai.
Ya bukaci al’ummar yankin su ƙara ƙoƙarin kusantar sauran ’yan Najeriya domin ƙulla alaƙa da haɗin gwiwa.
Shettima ya kwatanta Obi da Buhari
Yayin da yake magana kan farin jinin Peter Obi, Shettima ya ce Buhari ya taɓa samun gagarumin goyon baya a Arewa, amma hakan bai wadatar wajen ba shi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa ba.

Kara karanta wannan
Magana ta kare: Jam'iyyar adawa ta yanke shawara, ta umarci mabiyanta su zaɓi Tinubu a 2027
“Kada ku bari wani ya gaya muku cewa al’ummar Igbo ba su da muhimmanci a tsarin Najeriya. Ina so in gaya muku cewa akwai ’yan Igbo miliyan 17 da ke zaune a Arewacin Najeriya, sannan akwai miliyan 10 a Legas kaɗai. Na san suna da damar zuwa nan. Dole ne ku kai musu ziyara ku ƙulla alaƙa da su.
“Peter Obi ba zai fi Muhammadu Buhari farin jini ba. Buhari ya yi ƙoƙarin zama shugaban Najeriya a shekarar 2003, alhali ya taɓa zama shugaban ƙasa na mulkin soja. Ya sake tsayawa takara a 2007, amma ya sha kaye.
“Ya sake tsayawa takara a 2011, duk da cewa yana da ƙaƙƙarfan goyon bayan ƙuri’u miliyan 15 a Arewacin Najeriya, amma bai yi nasara ba.
“Dalili kuwa shi ne, samun ƙaƙƙarfan goyon baya a faɗin ƙasa shi ne abin da ake buƙata domin lashe zaɓen shugaban ƙasa a ƙasa irin Najeriya.
“Ina gaya muku, mu kasance masu gaskiya da juna. Mu tattauna da mutane, mu yanke shawara bisa ingantattun bayanai, domin hakan zai amfani Najeriya.” In ji shi.

Source: Facebook
Shettima ya soki Amaechi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Kashim Shettima, ya soki Rotimi Amaechi, kan zargin cewa marigayi Muhammadu Buhari ya yi masa alƙawarin tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a 2023, amma daga baya ya karya alƙawarin.
Shettima ya bayyana zargin dan takarar mataimakin shugaban kasar na ADC a matsayin magana marar dacewa da rashin girmamawa ga marigayi Buhari.
Asali: Legit.ng