Mata na cikin Alheri, An Fara Raba Tallafin N50,000 ga Wadanda Suka Cancanta a Jihar Kano
- Gwamnatin jihar Kano ta raba tallafin Naira miliyan 290 ga mata 5,800 a kananan hukumomi 44 domin fargadi da sana'o'in su
- Rahotanni sun nuna cewa kowace mace daga cikin matan za ta samu N50,000 domin fara ko fadada sana'arta
- Gwamna Abba Oabir Yusuf ya ce za a ci gaba da biyan tallafin da wadanda suka cancanta har zuwa watan Disamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da fara rabon tallafin Naira miliyan 290 ga mata 5,800 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
An bayar da tallafin ne karkashin shirin gwamnati na karfafa mata da rage talauci da ake gudanarwa duk wata.

Source: Facebook
Gwamna Abba Yusuf ya kaddamar da sabon zagaye na shirin a Open Arena da ke gidan gwamnatin Kano ranar Litinin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka
Ya ce kowace daga cikin matan da za su amfana da shirin za ta samu N50,000 domin fara sabuwar sana'a ko fadada wadda take yi.
Yadda za a raba tallafin ga matan Kano
Gwamna Abba ya bayyana cewa an gayyaci kashi 20 cikin 100 na wadanda suka amfana daga kowace karamar hukuma domin halartar bikin kaddamar da shirin.
Ya ce sauran kashi 80 cikin 100 za su karbi tallafinsu a kananan hukumominsu.
"Yau muna kaddamar da tallafi ga mata 5,800 daban-daban. Daga cikin wadannan mata 5,800, mun zabo kashi 20 daga kowace karamar hukuma domin halartar wannan bikin kaddamarwa.
"Gobe, kowane shugaban karamar hukuma da mambobin kwamitinsa za su koma kananan hukumominsu domin raba tallafin ga sauran kashi 80."
Gwamna Abba ya yi bayani kan shirin
Gwamna Abba ya ce shirin karfafa mata ya fara tun bayan hawansa mulki, sai dai ya ce an dakatar da shi na wani dan lokaci yayin sauyin gwamnatin zuwa jam'iyyar APC.
A cewarsa, an dakatar da shirin ne domin sake tsara shi tare da tabbatar da cewa matan da suka yi rajista tun farko, da kuma wadanda suka shiga APC, sun shiga cikin wadanda za su amfana.
Gwamnan ya tabbatar wa mata cewa gwamnati ta ware kudaden da za a ci gaba da gudanar da shirin, yana mi cewa za a ci gaba da biyan tallafin har zuwa watan Disamba.
Gwamna Abba Yusuf ya bukaci wadanda suka amfana da tallafin su yi amfani da kudaden wajen sana'o'in da za su amfane su.

Source: Facebook
Ya ba da misalin kananan sana'o'i da kasuwanci, musamman sayar da kayan masarufi da abinci. Ya ce hakan zai taimaka wa matan wajen dogaro da kansu tare da tallafa wa iyalansu.
Gwamnan ya kuma nemi mata su goyi bayan 'yan takarar APC a zaben 2027, inda ya bukace su da su zabi 'yan takarar shugaban kasa, gwamna, majalisar tarayya da majalisar dokokin jiha na APC.
Wata matar aure da ta taba amfana da shirin tallafin mata na gwamnatin Kano, Ummahanu Sulaiman ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa tallafin na taimakonsu matuka.
Ta ce ta samu kusan miliyan daya da Abba ya bai wa wasu kungiyoyin kungiyoyi tallafin kama sana'ar da ta shafi noma kuma tun daga lokacin rayuwarta ta canza.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya yi magana mai tsauri kan kisan fitaccen mai sharhi kan siyasa a Kano
Mstar ta ce:
"Akwai mata da yawa da jari kawai suke bukata, suna da sana'a amma yau da kullum ta sa ta durkushe, da an dan daga su za su tashi. Ina cikin matan da suka amfana kuma mijina kansa yana amfana da sana'a ta."
Abba ya ba da kwangilolin kusan N1trn
Kun ji cewa gwamnatin Kano ta ce ta ba da kwangilolin ayyuka na N996.29bn a karkashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf, inda aka kammala ayyuka 867 a fadin jihar.
Gwamnatin ta kuma ce ba ta karbo ko sisi a matsayin bashi, daga cikin gida ko wajen Najeriya, domin daukar nauyin ayyukan da aka aiwatarnba, yayin da aka soke kwangiloli biyar saboda karya yarjejeniya
Asali: Legit.ng
