Gwamna Abba Ya Yi Magana Mai Tsauri kan Kisan Fitaccen Mai Sharhi kan Siyasa a Kano
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da kisan gillan da aka yi wa fitaccen dan soshiyal midiya Ibrahim Khalil, wanda aka fi sani da Danshagamu
- Gwamnan ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta gano tare da kama wadanda ke da hannu a kisan domin doka ta yi aiki a kansu
- Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su kwantar da hankula, tare da kauce wa ɗaukar doka a hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria – Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa fitaccen mai amfani da kafafen sada zumunta kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Ibrahim Khalil, wanda aka fi sani da Danshagamu.
Gwamna Abba ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta gano tare da kama dukkan wadanda suke da hannu a aikata kisan domin a gurfanar da su a gaban doka.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Laraba, 9 ga watan Satumba, 2026.
Yan uwa marigayin sun ce wasu mutane da har yanzu ba a gano su ba sun kai wa marigayin hari bayan sun kutsa gidansa, inda suka yanka shi har lahira.
Rundunar yan sandan Kano ta ce ta kama mutum biyu da ake zargin sune suka kashe Danshagamu.
Gwamna Abba ya yi magana
Sai dai da yake martani, Gwamna Abba ya bayyana kisan a matsayin abin ban tsoro da ba za a amince da shi ba, yana mai nuna damuwa kan yanayin da lamarin ya faru.
Ya kuma bukaci a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda ke da hannu a lamarin a gaban kuliya.
Gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da abokansa da kuma abokan hulɗarsa, yana addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya kuma ba shi hutawa ta har abada.
Gwamna ya kwantar da hankulan jama’a
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar Kano da su kwantar da hankula tare da kauce wa ɗaukar doka a hannu.
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatin za ta ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

Source: Facebook
Haka kuma, Gwamna Abba ya umarci hukumomin tsaro da abin ya shafa, musamman Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ’yan sandan Najeriya na jihar Kano, da su ƙara kaimi wajen gano, kama da gurfanar da wadanda suka aikata kisan.
Ya jaddada cewa ba za a bari wani mutum ko wata ƙungiya ta ɗauki doka a hannunta ba.
Kwankwaso ya bukaci a dauki mataki
Kun ji cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana matuƙar damuwarsa kan kisan shahararren mai sharhin siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu.
Ya ce Dan Shagamu ya mutu ne sakamakon mummunan hari, inda ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta gaggauta kafa kwamitin bincike domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Asali: Legit.ng

