Dalung Ya Ja Hankalin Rarara bayan Lakada Masa Duka a Abuja

Dalung Ya Ja Hankalin Rarara bayan Lakada Masa Duka a Abuja

  • Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya yi Allah-wadai da rahoton dukan mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, a masallacin Abuja
  • Dalung ya ce babu wanda ya cancanci a kai masa hari saboda ra’ayinsa na siyasa ko goyon bayan gwamnatin da yake so
  • Ya bukaci Rarara ya yi tunani kan halin da talakawan Najeriya ke ciki, musamman matsin tattalin arziki da suka danganta da manufofin gwamnatin da yake yabawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya yi martani kan rahotannin cewa wasu fusatattun matasa sun lakadawa fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, duka bayan sallar Juma’a a Abuja.

Dalung ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa babu wanda ya kamata a kai wa hari ko cin zarafi saboda ra’ayinsa na siyasa ko goyon bayan wata gwamnati.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnoni za su jawo jama'a a jiki bayan wahalar cire tallafin mai

Solomon Dalung
Tsohon minista, Solomon Dalung. Hoto: Solomon Dalung
Source: Getty Images

A sakon da ya wallafa a Facebook, tsohon ministan ya ce lamarin ya kamata ya zama darasi ga Rarara, musamman yadda mawakin ya shafe shekaru yana wakokin yabon shugabannin siyasa, musamman wadanda ke kan mulki.

Dalung ya yi tir da dukan Rarara

Dalung ya bayyana cewa rashin jituwa kan siyasa bai kamata ya zama dalilin kai wa mutum hari ko amfani da karfi wajen tsoratar da shi ba.

Ya ce idan mutane ba su amince da ra’ayin siyasar wani ba, ya kamata su kalubalanci ra’ayinsa da hujjoji maimakon yin amfani da duka.

Tsohon ministan ya jaddada cewa Rarara na da ‘yancin yin wakoki ga Shugaba Bola Tinubu, jam’iyyar APC ko duk wata kungiya ta siyasa da yake so.

Haka kuma, ya ce sauran ‘yan Najeriya na da ‘yancin nuna rashin amincewarsu da gwamnati ko kuma su yi tambayoyi kan sakonnin da mawakin ke isarwa ta wakokinsa.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya yi wa gwamna Abba Kabir tayin mata

Batun halin da talakawa ke ciki

Dalung ya bayyana cewa akwai ‘yan Najeriya da dama da ke fama da matsin tattalin arziki, inda wasu iyaye ke kokarin samar da abinci ga iyalansu, yayin da matasa da suka kammala karatu ke fama da rashin aikin yi.

Ya kuma yi nuni da kananan ‘yan kasuwa da ke kokarin kare jarinsu sakamakon tsadar kayayyaki, sufuri, wutar lantarki da sauran bukatun yau da kullum.

A cewarsa, yayin da talakawa ke fuskantar wadannan matsaloli, akwai masu ganin cewa manufofin tattalin arzikin gwamnati na kara musu nauyi, yayin da wasu ‘yan siyasa ke ci gaba da yabon shugabannin da ke kan mulki.

Dalung ya ce bai kamata a dauki yadda ake taya ‘yan siyasa murna a wajen taruka a matsayin hujjar cewa dukkan al’ummar Najeriya sun amince da shugabancinsu ba.

Dauda Kahutu Rarara
Mawakin APC. Dauda Rarara. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Facebook

Shawarar Dalung ga Rarara

Ya kuma bayyana fatan Rarara zai warke daga abin da ya faru, yana mai cewa ya kamata mawakin ya yi tunani kan wahalhalun da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon halin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Yadda rikici ya kaure tsakanin na hannun daman Tinubu da gwamnan APC

A cewarsa, ba kowa ne ke da damar bayyana damuwarsa ta amfani da makirufo ba, domin wasu na kokarin neman yadda za su tsira da rayuwarsu ne kawai.

An yi wa Kwankwaso ba dadi

A wani labarin, mun rahoto cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin jihar Gombe da matsa wa masu wani wurin taro lamba, lamarin da ya tilasta sauya wurin gudanar da taron.

Kwankwaso, wanda ke takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar NDC, ya jagoranci taron tattaunawa da al’ummar Gombe a ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026.

Jagoran Kwankwasiyya ya kuma gana da ‘yan takarar jam’iyyar a jihar, tare da karbar ziyarar dattawan kungiyar ci gaban Yamaltu Deba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng