‘Abin da Ya Sa Bai Kamata a Aminta da Pantami Ya Mulki Jihar Gombe ba’

‘Abin da Ya Sa Bai Kamata a Aminta da Pantami Ya Mulki Jihar Gombe ba’

  • Tsohon Sakataren NUJ a Gombe, Danjuma Kala, ya nuna damuwa kan cancantar Isa Ali Pantami ya zama gwamnan Gombe
  • Kala ya ce yadda Pantami ya samu matsayin farfesa na bukatar bincike sosai, musamman kan bin ka’idojin jami’a da ingancin tsarin nadin.
  • Ya bukaci masu zaɓe a Gombe su duba tarihin ‘yan takara da yadda suka samu ci gaba, kafin su yanke hukunci kan zaɓen 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Tsohon Sakataren-Janar na Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Najeriya, NUJ, reshen Gombe, Danjuma Kala, ya caccaki Farfesa Isa Ali Pantami.

Kala ya nuna shakku kan cancantar Farfesa Isa Ali Pantami ya jagoranci Gombe yayin da ake shirin zaben 2027.

An sake taso Pantami a gaba kan karatunsa
Dan takarar gwamnan PDP a Gombe, Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Kala ya bayyana haka a wani rubutu mai taken, “Dalilin da ya sa bai kamata a amince wa Pantami da mulkin Gombe ba: 2027,” wanda Punch ta samu.

Kara karanta wannan

Wa ya fi gaskiya tsakanin El Rufai da ministan tsaro? Dattawan Arewa sun magantu

An shawarci binciken tarihin karatun yan takara

A cikin rubutun, ya ce tarihin karatu da na hukumomin ‘yan takarar siyasa ya kamata a bincika sosai kafin a ba su amanar mulkin jama’a.

A cewarsa, ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan ɗaga Pantami zuwa matsayin farfesa ya haifar da tambayoyi kan gaskiya, rikon amana da bin ƙa’idojin hukumomi.

Kala ya ce masu zaɓe a Gombe ya kamata su duba ba kawai alkawuran ‘yan takarar gwamna ba, har ma da tarihinsu da yadda suka samu ci gaba a sana’arsu.

Ya ce:

“Tambayar ba ita ce ko an yi amfani da ikon fasaha ba, sai dai ko an bi tsarin hukumomi yadda ya kamata, cikin gaskiya da bin ƙa’idojin da aka kafa.
“Jagoran da ya nuna yana son samun ci gaba ta hanyoyin da ke da manyan matsalolin rashin bin ƙa’ida, yana nuna yadda zai iya tafiyar da mulki.”

Ya bayyana cewa ikon naɗa farfesa yana hannun majalisar gudanarwar jami’a, yana mai cewa Majalisar Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri ce ta kula da naɗin Pantami.

Kara karanta wannan

Dalung ya jefawa Christopher Musa tambayoyi kan zargin Nasir El Rufa'i

Ana zargin tarihin karatun Isa Ali Pantami
Taswirar jihar Gombe da Isa Pantami ke neman takara karkashin PDP. Hoto: Legit.
Source: Original

'Har yanzu ba a soke nadin Pantami ba'

Kala ya ce binciken ASUU da aka fitar a shekarar 2021 ya kamata a yi la’akari da shi, saboda ya nuna shakku kan bin ƙa’idojin karatu da tsarin da aka saba wajen naɗin farfesa.

Sai dai ya amince cewa matsayin Pantami na farfesa yana nan daram, saboda a cewarsa, majalisar gudanarwar jami’ar ba ta soke naɗin a hukumance ba, cewar Daily Pots.

Ya ce:

“Tambayar da ya kamata masu zaɓe su yi ba ita ce ko majalisar gudanarwar jami’ar tana da ikon yin naɗin ba. Tambayar ita ce ko an yi naɗin ta hanyar da ta dace da gaskiyar hukumomi da bin ƙa’idojin da aka kafa.”

Tsohon jami’in NUJ ɗin ya kuma yi zargin cewa Pantami yana da kusan shekara guda kacal na koyarwa bayan kammala digirin digirgir a lokacin da aka naɗa shi farfesa.

Shugaban matasan PDP ya bar jam'iyyar a Gombe

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya jero masu amfana da cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi

Mun ba ku labarin cewa shugaban matasan PDP na Jihar Gombe, Jamilu Ali Kalshingi, ya yi murabus daga mukaminsa da kuma kasancewarsa ɗan jam’iyyar.

Kalshingi ya ce ya ɗauki matakin ne bayan yin dogon tunani, kuma murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take.

Murabus ɗin ya zo ne jim kaɗan bayan tsohon ma’ajin PDP na ƙasa, Ahmed Yayari, ya sauya sheƙa zuwa sansanin ɗan takarar gwamnan APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.