Kwankwasiyya Ta Fallasa Shirin da Aka Yi Wajen Tarbar Dumbin Mutane zuwa APC a Kano
- Kwankwasiyya ta ce sauya sheƙar ’yan siyasa da magoya baya zuwa APC a Kano ba za ta shafi damar ta na lashe zaɓen 2027 ba
- Kakakin ƙungiyar ya yi watsi da rahoton cewa mutane sama da 130,000 ne suka koma APC, yana mai cewa an yi karin gishiri a zancen
- Ya ce ƙarfin Kwankwasiyya ya samo asali ne daga magoya bayanta na ƙasa, ba daga ’yan siyasar da ke riƙe da mukamai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Ƙungiyar Kwankwasiyya ta ce sauya sheƙar wasu ’yan siyasa da magoya baya zuwa jam’iyyar APC a Jihar Kano ba za ta shafi damar da take da ita ta lashe zaɓen 2027 ba.
Kakakin ƙungiyar, Habibu Mohammed, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, 6 ga watan Satumban 2026 yayin da yake mayar da martani kan rahoton sauya sheƙar mutane sama da 130,000 daga jam’iyyun siyasa daban-daban zuwa APC.

Source: Facebook
Kwankwasiyya ta yi watsi da adadin
Mohammed ya yi magana ne a wata hira ta musamman da jaridar Leadership, inda ya yi watsi da adadin mutanen da aka ce sun koma APC.
Ya yi zargin cewa an yi karin gishiri kan adadin, yana mai cewa babban dalilin taron shi ne nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma nuna ƙarfin siyasar gwamnatin Kano.
Ya kuma ce sauya sheƙar wasu fitattun ’yan gidan siyasar Kwankwasiyya ba za ta raunana ƙungiyar ba, domin ƙarfin ta ya samo asali ne daga magoya bayanta a matakin ƙasa.
Ya ce Kwankwasiyya ce ke gina ’yan siyasa
Kakakin ya ce ficewar duk wani mai riƙe da mukamin siyasa a cikin Kwankwasiyya ko gwamnati ba zai sauya damar ƙungiyar ta samun nasara a zaɓe ba.
“Sauya sheƙar duk wani mai riƙe da mukamin siyasa a Kwankwasiyya ko gwamnati daga Kwankwasiyya ba zai sauya ko shafar damar Kwankwasiyya ta yin nasara ba."

Kara karanta wannan
Rashin tsaro: Janar Musa ya ce Najeriya ta yi galaba kan 'yan ta'adda, ya gabatar da dalili
“Kwankwasiyya ba a taɓa gina ta a kan waɗannan mutane ba. A koyaushe Kwankwasiyya ce ke ɗaga waɗannan mutane, ba akasin haka ba,” in ji shi.
Ya ce akwai ’yancin barin ƙungiyar
Mohammed ya ce mutanen da ba su jin daɗin bin ƙa’idojin da manufofin Kwankwasiyya ba suna da ’yancin barin ƙungiyar.
Sai dai ya ce ficewarsu ba za ta lalata tushen goyon bayan da ƙungiyar ke da shi a zaɓe ba.
A cewarsa, Kwankwasiyya ta samo asali ne daga burin talakawa, waɗanda a ƙarshe su ne ke da ikon yanke shawarar wanda zai yi nasara a zaɓe.
Ya tuna da zaɓen da ya gabata
Kakakin Kwankwasiyya ya tuna cewa ƙungiyar ta samu sama da ƙuri’u miliyan ɗaya a Kano a zaɓen da ya gabata.
Ya ce yawan mutanen da suka halarci taron APC ba zai yiwu a kwatanta shi da dumbin magoya bayan Kwankwasiyya da ke matakin ƙasa ba.
Mohammed ya kuma yi zargin cewa an kwaso wasu daga cikin mahalarta taron APC daga wurare daban-daban, sannan aka ba su kuɗi domin su halarci taron.

Kara karanta wannan
Shin da gaske Sheikh Gumi ya yi barazanar hargitsa Najeriya kan 'yan bindiga? An gano gaskiya
Ya ce talakawa ne ke yanke hukunci
Mohammed ya ce ƙuri’un talakawa ne ke ƙayyade wanda zai yi nasara a zaɓe, yana mai cewa magoya bayan Kwankwasiyya sun yi imanin cewa burinsu zai iya cika ne ta hanyar ƙungiyar.
“Talaka ne ke kaɗa ƙuri’a, kuma su ne ke yanke shawara bisa burin da suka yi imanin cewa Kwankwasiyya ce kaɗai za ta iya cika shi, ba tare da la’akari da wanda ke jagorantar ta ba,” in ji shi.
Kwankwasiyya ta ƙara jaddada kwarin gwiwa
Kakakin ƙungiyar ya bayyana cikakken kwarin gwiwar cewa Kwankwasiyya za ta riƙe tushen goyon bayan da take da shi a Kano.
Ya kuma ce ƙungiyar na da yakinin cewa za ta samu nasara a zaɓen 2027 a jihar, duk da sauya sheƙar wasu ’yan siyasa da aka samu zuwa APC.

Source: Facebook
Kwankwaso ya ce gwamnoni sun gaza
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya yi gargadin cewa yan Najeriya sun fusata da wasu daga cikin shugabanninsu musamnan gwamnoni.
Kwankwaso ya ce gwamnoni da dama, musamman wadanda ke Arewacin Najeriya, sun yi abin da ya bayyana a matsayin rashin kyakkyawan aiki da gazawa.
Asali: Legit.ng
