NDC: Mutanen Gawuna za Su Rabu da Kwankwaso Su Koma wajen Abba a APC

NDC: Mutanen Gawuna za Su Rabu da Kwankwaso Su Koma wajen Abba a APC

  • Tawagar tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ta kai ziyarar girmamawa ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Murtala Sule Garo
  • Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin komawar wasu daga cikin magoya bayan Yusuf Gawuna zuwa jam’iyyar APC daga NDC
  • Hon. Muhammad Badaru Umar da Mataimakin Shugaban NDC na Jihar Kano, Hon. Ali Datti Yako, ne suka jagoranci tawagar a ziyarar da suka kai wa Abba Kabir Yusuf

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Tawagar tsohon Mataimakin Gwamnan Kano kuma ɗan takarar gwamna na APC a zaɓen 2023, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ta kai ziyarar girmamawa ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da mataimakinsa, Murtala Sule Garo.

Ziyarar ta zo ne yayin da ake shirin komawar wasu daga cikin magoya bayan Gawuna zuwa jam’iyyar APC daga NDC.

Kara karanta wannan

Najeriya ta tafka rashi, Allah ya yi wa mai martaba Sarkin Zurmi rasuwa

Abba Kabir Yusuf da mutanen Gawuna
Tawagar gwamnatin Kano da jama'ar Yusuf Gawuna. Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa
Source: Facebook

Tawagar Gawuna ta ziyarci Abba

Hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature ne ya wallafa hotunan ziyarar a Facebook, inda ya bayyana cewa tawagar Gawuna ta kai wa gwamnan da mataimakinsa ziyarar haɗin kai.

An ce ziyarar ta gudana ne a yammacin ranar Talata, inda tawagar ta gana da Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa Murtala Sule Garo.

Hon. Muhammad Badaru Umar da Hon. Ali Datti Yako, Mataimakin Shugaban NDC na Jihar Kano, ne suka jagoranci tawagar.

'Yan Gawuna za su koma APC

Dr. Nasiru Yusuf Gawuna tsohon Mataimakin Gwamnan Kano ne, sannan ya kasance ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Gawuna ya koma NDC ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga NNPP ya koma APC, lamarin da ya kawo sauyi a tsarin siyasar Kano da kuma alaƙar siyasa tsakanin wasu daga cikin manyan jiga-jigan jihar.

Kara karanta wannan

Za a tura tawaga ga dattawan Igbo domin rokon Obi ya janye wa Tinubu a 2027

Yanzu dai ana shirin ganin wasu mutanen Gawuna sun sake komawa APC daga NDC, a wani mataki da zai iya yin tasiri a siyasar Kano gabanin zaɓen 2027.

Nasiru Yusuf Gawuna
Lokacin da Nasiru Gawuna ya sauya sheka. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

A yanzu haka dai Gawuna ya samu tikitin NDC na takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, inda aka cire sunan Sanata Rufai Sani Hanga daga takarar.

Jagoran ƙungiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ne ya sanar da zaɓen Gawuna a matsayin ɗan takarar NDC na Sanatan Kano ta Tsakiya.

Hanga ya zargi Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga, ya bayyana cewa rashin jituwarsa da Rabiu Musa Kwankwaso, ce ta kai ga rabuwar siyasarsu.

Sanatan ya ce Kwankwaso ya fara nuna rashin jin daɗi da shi ne bayan ya shirya wani gagarumin shirin tallafa wa al’ummar mazabarsa, inda ya raba motoci, shinkafa, taki, injinan niƙa da sauran kayayyaki.

Hanga ya ce rashin jituwar ta ƙara tsananta ne lokacin da ya gudanar da shirin a wani wuri da ke da alaƙa da Kwankwaso, bayan tsohon gwamnan ya amince da halartar taron domin ganin yadda ake raba kayan tallafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng