Iyaye Sun Shiga Ha’ula’i, ‘Yan Bindiga Sun Bukaci N950m kafin Sakin Masu NYSC

Iyaye Sun Shiga Ha’ula’i, ‘Yan Bindiga Sun Bukaci N950m kafin Sakin Masu NYSC

  • ‘Yan bindiga sun sace 'yan bautar kasa (NYSC) a makon nan a hanyar Owerri zuwa Onitsha a jihar Imo
  • Masu garkuwar suna bukatar har Naira miliyan 50 a kan kowane mutum daya a matsayin kudin fansar shi
  • Jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike domin ceto matasan, abokai kuma sun fara baran kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Imo - ‘Yan bindigan da suka dauke wasu matasa masu yi wa kasa hidima sun bukaci a biya kudin fansa kafin su sake su.

‘Yan bindigan sun tare motocin da ke dauke da fasinjoji ciki har da ‘yan NYSC din ne a a babban titin Owerri zuwa Onitsha.

'Yan NYSC
Wasu ‘yan NYSC a jihar Nasarawa (Ba su ne wadanda aka dauke ba) Hoto: NYSC Nasarawa State
Source: Facebook

Fansar N950m ta shiga tsakanin matasa da 'yan bindiga

Rahoto ya zo daga jaridar Punch cewa ‘yan bindigan sun sa kudin fansar wadannan matasa 19 kan Naira miliyan 950.

Kara karanta wannan

Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta

Shugaban kamfanin motocin haya na Uko Akwa Ibom Motors Nigeria Limited ya tabbatar da wannan labari a ranar Juma’a.

Isiah Akpan ya ce ‘yan bindigan sun nemi kowanne ya kawo N50m kafin a sake yin ido hudu da shi.

Labarin yadda aka dauke 'yan NYSC

Mista Isiah Akpan yake cewa fasinjojin da aka dauke masu yi wa kasa hidima ne da suke hanyar zuwa Abia da Akwa Ibom.

Shugaban kamfanin ya ce motocin sun bar tashar Bodija/Samonda ne tun ranar Laraba, amma aka samu matsala a Benin.

Lokacin da motocin suka isa birnin Onitsha a jihar Anambra, dare ya yi saboda haka dole suka hakura suka kwana a Oba.

Akpan ya ce da asubar Alhamis aka cigaba da tafiyar, amma kafin tafiya ta yi nisa a kai ga isa Imo, sai ‘yan bindiga suka tare su.

Direbobin sun yi nasarar tserewa kuma su ne suka ankarar da jami’an tsaro, amma an dauke duka matasan 19 da ke NYSC.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

'Yan bindiga sun kira iyayen 'yan NYSC

An fahimci ‘yan bindigan sun tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa, sun fada masu cewa kowa ya tanadi Naira miliyan 50.

Dole wannan ya jefa iyalai da danginsu cikin tashin hankali duk da jami’an tsaro sun ce suna kokarin gano inda aka kai su.

Wani daga cikin iyayen yaran ta ce an kira ta ta wayar ‘dan nata, aka fada mata cewa ta tanadi N50m kafin ta iya sake ganin shi.

Haka zalika wata uwar mai suna, Mrs Oladosu ta tabbatar da cewa an daike diyar ta, Greatness kuma an kira ta a wayar salula.

Ta ce har sun yi waya ta bidiyo amma an bukaci ta nemo N50m. a matsayinta na karamar ‘yar kasuwa, ta ce ba ta da dalilin su.

An fara neman kudin fansar matasan a X

Wasu a kafafen sada zumunta sun fara yunkurin tattaro kudi wajen jama’a a yanar gizo domin ganin sun fanso abokan nasu.

Kara karanta wannan

An kama shugaban ƙungiyar magoya bayan Peter Obi da Kwankwaso

Wani Adebayo (@Adebayoakim1), yana neman kudi domin a saki abokinsa, Wahab Ayandare.

Shi ma Akinlabi Abayomi (@Mubiiiiin) ya bi sahunsa a X, yana rokon mutane su hada masu kudi domin a fanshi Oyindamola Adeoye.

Cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su akwai Akande Kehinde, Olaleye Mary, Oladosu Greatness sai wani Obafunsho Rhoda.

Akwai Abdulrof Anifat, Esther Oyede, Hassan Usman, Ayomide Isa, Mary Makinde, Azeez Adejoke da kuma Abdulrazaq Anifat.

NYSC.
Wasu matasa da ke NYSC a Nasarawa da jami'in tsaro a kan titi Hoto: NYSC Nasarawa State
Source: UGC

'Yan sanda sun tabbatar da dauke masu NYSC

An samu labarin lokacin da aka ji 'yan bindiga sun yi garkuwa da matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) a Kudancin Najeriya.

Hukumar 'yan sanda tare da sauran jami'an tsaro sun dukufa domin ceto fasinjojin daga cikin jeji.

An ji cewa sun yi ikirarin ceto 'yan bautar kasa 10 daga cikin mutane 20 da aka sace a kan hanyar Owerri zuwa garin Onitsha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng