An Cafke Dan Sandan Bogi da Ya Shiga Kano Ya Rika Damfarar Jama'a

An Cafke Dan Sandan Bogi da Ya Shiga Kano Ya Rika Damfarar Jama'a

  • Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Adamu Musa, mai shekaru 35, bisa zargin yin karyar babban jami’in ’yan sanda da damfarar jama’a
  • Ana zargin mutumin da yin amfani da hotunan da aka hada fasahar AI wajen yaudarar mutane cewa yana da iko wajen samun guraben aikin ’yan sanda
  • ’Yan sanda sun kwato kayan sawa na jami’an tsaro da kuma N300,000 daga hannun wanda ake zargin yayin binciken gidansa kuma sun fadi matakin da za su dauka a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Adamu Musa, mai shekaru 35, mazaunin unguwar Kureken Sani a Kano, bisa zargin yin karyar shi babban jami’in dan sanda ne.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bindige babban manajan banki a Najeriya har ya mutu

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar 8 ga Satumba, 2026.

Dan sandan bogi a Kano
Wanda aka kama da kayan 'yan sanda a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kiyawa ya wallafa a Facebook cewa an kama wanda ake zargin ne bayan rundunar ta samu rahoton gaggawa daga Rundunar ’Yan Sandan da ke Challawa, Kano, a ranar 1 ga Satumba da misalin ƙarfe 7:30 na dare.

An kama dan sandan bogi

Bayan samun sahihan bayanan sirri, jami’an sashen ’yan sanda na Panshekara sun gudanar da samame tare da cafke Adamu Musa.

Rundunar ta ce wanda ake zargin ya kasance yana yawo yana gabatar da kansa a matsayin Babban Sufeto na ’Yan Sanda, wato CSP.

Binciken farko ya nuna cewa mutumin ya ƙware wajen damfarar mutanen da ba su san gaskiyar lamarin ba, ta hanyar nuna cewa shi babban jami’i ne mai tasiri a harkar ɗaukar ’yan sanda aiki da kuma sauya wuraren aikinsu.

Kara karanta wannan

Bayani dalla dalla kan yadda za ku saye hannun jari a matatar Dangote

Dan sandan bogi na aiki da AI

Rundunar ta ce domin ya sa damfararsa ta yi kama da gaskiya, wanda ake zargin ya riƙa yaɗa hotunan kansa da aka gyara ta hanyar fasahar zamani.

An ce wasu daga cikin hotunan an ƙirƙire su da fasahar AI, inda aka haɗa hotonsa da na manyan kwamandojin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya.

Ana zargin ya riƙa amfani da waɗannan hotuna tare da sunayen manyan jami’ai wajen yaudarar mutane cewa zai iya samo masu guraben aikin ’yan sanda ko kuma sauya masu wuraren aiki idan sun biya kuɗi.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Kayan da aka samu a wajensa

A yayin binciken gidan wanda ake zargin, jami’an ’yan sanda sun kwato abubuwa da dama da ake ɗauka a matsayin hujjoji.

Daga cikin abubuwan da aka kwato akwai riga da wando na kayan ’yan sanda guda ɗaya, takalma guda biyu, rigar jami’an ’yan sanda shuɗi guda ɗaya.

Kara karanta wannan

Jirgin sojoji ya saki bama bamai a Zamfara, an kashe Kachalla Gurgu

Wasu rahotanni sun kara da cewa jami’an 'yan sanda sun yi nasarar kwato kuɗi har N300,000 a wajen dan sandan bogin.

An kama barayin yara

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta bankado wata ƙungiyar da ake zargi da satar yara da safarar mutane tsakanin jihohi.

Binciken ya samo asali ne daga wata ƙara da Adejoke Popoola, wadda aka fi sani da Orente Alagbo, ta shigar a ranar 29 ga Yuli, 2026 kan wasu zarge-zarge.

Yayin da jami’an rundunar ke binciken lamarin, hankalinsu ya karkata kan batan wani yaro mai shekaru uku mai suna Ifakunle Ifagbenro, wanda ya bace a ranar 29 ga Yuni, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng