APC Ta Shiga Matsala, Manyan Jam'iyya Sun Fita za Su Fara Adawa da Tinubu
- Jiga-jigan jam’iyyar APC a Bauchi sun ci gaba da ficewa daga jam’iyyar duk da kokarin sasanta rikicin da ya biyo bayan zaɓen fitar da gwani na 2027
- Daga cikin wadanda suka fice akwai tsohon mataimakin gwamnan jihar, Sagir Saleh, da tsohon mai neman takarar gwamnan APC har sau biyu, Bala Jibrin
- Sun zargi shugabancin APC da rashin adalci, rashin bin tsarin dimokuraɗiyya a cikin gida da kuma tilasta ‘yan takara yayin zaɓen fitar da gwani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Tsohon mataimakin gwamnan Bauchi, Sagir Saleh, da wasu manyan ‘yan jam’iyyar APC sun yi murabus daga jam’iyyar yayin da kokarin sasanta rikicin cikin gida ke ci gaba.
Saleh, wanda ya kasance mataimakin gwamna a lokacin mulkin tsohon gwamna Isa Yuguda, ya sanar da murabus dinsa a wata wasika mai kwanan wata 19 ga Agusta 2026.

Source: Twitter
Punch ta ce a wasikar da aka aika wa shugaban APC na Katagum ta hannun shugaban jam’iyyar na Matsango da ke Azare, ta bayyana cewa ya bar jam’iyyar ne saboda wasu dalilai na kashin kansa.
Bala Jibrin ya fita daga APC
Shi ma Bala Jibrin, tsohon mai binciken kudi na jam’iyyar CPC kuma wanda ya nemi takarar gwamnan Bauchi a karkashin APC sau biyu, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.
Jibrin ya bayyana hakan ne a wata wasika mai kwanan wata 31 ga Agusta 2026, wadda ya aika wa shugaban APC na Nasarawa/Bakin Kasuwa da ke Azare, Karamar Hukumar Katagum.
Ya ce murabus dinsa da janye goyon bayansa ga jam’iyyar za su fara aiki nan take, yana mai danganta matakin da abin da ya kira “babban rashin adalci” da kuma tilasta ‘yan takara ba tare da la’akari da ra’ayin ‘yan jam’iyyar ba.
Maganar zaben Tinubu da MA
Da yake magana da ‘yan jarida ta wayar tarho bayan murabus dinsa, Jibrin ya ce bai ga wani dalili mai karfi da zai sa ya ci gaba da zama a APC ba, wadda ya zargi da kasa fifita jin dadin talakawan Najeriya.
Ya kuma ce ba zai goyi bayan Shugaba Bola Tinubu ko Muhammad Abubakar a zaɓen 2027 ba, yana zargin cewa dukkansu sun gaza nuna isasshen kulawa ga jin dadin jama’a.

Source: Facebook
Sunusi Kunde ya fita daga APC
Haka kuma, Sunusi Kunde, wani makusancin Ministan Lafiya na kasa, Farfesa Ali Pate, ya sanar da ficewarsa daga APC.
Kunde ya aika da wasikar murabus dinsa ga shugaban jam’iyyar APC na Beti a Karamar Hukumar Misau, inda ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar “cikin tsananin damuwa.”
Martanin jam'iyyar APC
Da yake mayar da martani kan ficewar, Sakataren Yada Labarai na APC a jihar Bauchi, Shehu Dauda, ya ce ba abin mamaki ba ne jam’iyyun siyasa su fuskanci sabani da kalubale lokaci zuwa lokaci.
Dauda ya shaida wa ‘yan jarida cewa kowane mutum na da ‘yancin bayyana ra’ayinsa da kuma yanke shawarar makomarsa ta siyasa.
Shugaban APC ya nemi afuwa
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban APC a jihar Yobe, Muhammad Gadaka, ya janye kalaman da ya yi na cewa matan da mazajensu suka hana su kada kuri’a ga APC a zaben 2027 su kashe aurensu.
Gadaka ya kuma nemi afuwar jama’a, yana mai cewa kalaman nasa wasa ne kawai, ba wai yana nufin ya karfafa wa matan aure gwiwar su rabu da mazajensu ba.
Ya ce ya janye maganar da ya yi cewa duk matar da mijinta ya hana ta kada kuri’a ga APC ta kawo karshen aurenta, yana mai cewa ya yi wannan furucin ne a matsayin wasa.
Asali: Legit.ng


