2027: An Samu Babbar Matsala a Yunkurin Fitar da Dan Takara 1 tsakanin Atiku, Peter Obi da Makinde
- Yunkurin kungiyar G-100 na tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya na jam'iyyun adawa na fuskantar sabon kalubale
- Atiku Abubakar, Peter Obi da Seyi Makinde sun ci gaba da nuna cewa ba su janye daga neman kujerar shugaban kasa ba
- Wakilan jam'iyyun adawa sun ce ana ci gaba da tattaunawa domin cimma matsaya kafin karshen watan Satumba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Yunkurin kungiyar G-100 na tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya kafin zaben 2027 na iya fuskantar sabon cikas bayan Atiku Abubakar, Peter Obi da Seyi Makinde sun dage kan aniyarsu ta tsayawa takara.
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar ADC Peter Obi na NDC da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo na APM sun ci gaba da nuna cewa suna da burin neman kujerar shugaban kasa.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tafka kura kurai a gwamnati, ana ganin za su jawo ya sha kaye a zaben 2027

Source: Facebook
Punch ta ruwaito cewa wani mamba a G-100, Ambasada Umanu Elijah, ya nuna kwarin gwiwar cewa za a kammala shawarwari tare da cimma matsaya kan dan takarar bai daya kafin ranar 30 ga watan Satumba.
G-100 na neman dan takara guda
G-100 hadaka ce ta kungiyoyin siyasa da masu ruwa da tsaki da ke fafutukar ganin jam'iyyun adawa sun hada kai domin fuskantar zaben 2027.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa sansanonin Atiku, Obi da Makinde ba su nuna shirin janye wa wani daga cikinsu hanya ba.
Maimakon haka, kowannensu ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin dan takarar da ya dace, lamarin da ya kara jefa shakku kan yiwuwar tsayar da dan takara guda.
Atiku bai janye daga takarar ba
Mai taimaka wa tsohon mataimakin shugaban kasa wajen hulda da kafafen yada labarai, Paul Ibe, ya ki yin tsokaci kan batun.
Sai dai wani na kusa da Atiku ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ba ya adawa da kafa hadaka tsakanin jam'iyyun siyasa.
Majiyar ta ce Atiku ya dade da tunanin kafa hadakar 'yan adawa, kuma wannan ne ya haifar da samuwar ADC a matsayin dandali na wasu shugabannin adawa.
Sai dai ta jaddada cewa Alhaji Atiku Abubakar zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027, tana mai cewa masu ganin shi ne ya fi cancanta za su iya mara masa baya daga sauran jam'iyyun siyasa.
APM ta jaddada goyon bayan Makinde
Sakataren yada labarai na kasa na APM, Abubakar Yusuf, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsu, Gwamna Seyi Makinde, bai fice daga takarar 2027 ba.
Yusuf ya shaida wa Punch cewa Makinde ya shiga takarar ne domin yin nasara, ba kawai domin shiga zaben ba.
Ya ce:
"Gwamnan jihar Oyo, wanda shi ne dan takarar jam'iyyarmu, bai shiga wannan takara domin yaudarar 'yan Najeriya ko wasa da barkwanci ba. Ya shiga takarar ne domin yin nasara. Yana neman nasarar zaben 2027."

Source: Facebook
NDC ta nemi a zabi Peter Obi
Sakataren yada labarai na kasa na NDC, Osa Director, ya ce jam'iyyarsa a bude take wajen tattaunawa kan tsayar da dan takarar shugaban kasa guda ga jam'iyyun adawa.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya bada mamaki, ya halarci ƙaddamar kamfe na wani ɗan takarar shugaban kasa a 2027
Ya ce dan takarar jam'iyyar yana daga cikin manyan masu damar zama zabin hadakar.
Osa ya ce NDC a shirye take ta shiga tattaunawar samar da dan takara guda tsakanin jam'iyyun adawa.
Ya ce jam'iyyar ta riga ta shiga irin wadannan mataki saboda ta yi imanin cewa dan takararta yana daga cikin mafiya cancanta kuma yana da babbar damar zama zabin hadakar jam'iyyun adawa.
APC ta soki shirin hadakar yan adawa
Kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta yi watsi da taron jam'iyyun adawa, tana mai cewa yunƙurinsu ba zai kai ga nasara ba.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce taron ya nuna fargabar da ke tattare da 'yan adawa kan abin da yake ganin zai zama mummunar shan kashi a babban zaben 2027.
Asali: Legit.ng
