Peter Obi Ya bada Mamaki Ya Halarci Kaddamar Kamfe na Wani Dan Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, ya halarci taron kaddamar da yakin neman zaben dan takarar APM, Gwamna Seyi Makinde
- Obi ya isa wajen taron da misalin karfe 12.31 na rana yayin da ke dana da fara yakin neman zaben Gwamna Makinde na jihar Oyo
- Har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa Peter Obi ya halarci taron ba yayin da ake ci gaba da gudanar da shi a yau Litinin, 7 ga Satumba, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya halarci taron kaddamar da yakin neman zaben dan takarar APM a zaben shugaban kasa na 2027, Seyi Makinde.
Rahotanni sun nuna cewa Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, ya isa wajen taron da misalin karfe 12.31 na rana yau Litinin, 7 ga watan Satumba, 2026.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tafka kura kurai a gwamnati, ana ganin za su jawo ya sha kaye a zaben 2027

Source: Twitter
Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito cewa har yanzu ba a bayyana manufarsa ta halartar taron ba yayin da ake ci gaba da gudanar da shi.
Ana sa ran Makinde zai kaddamar da ofishin yakin neman zabensa a matsayin wani bangare na shirye-shiryen taron.
Wannan na zuwa ne yayin da yan adawa ke kokarin dunkulewa wuri guda tare da tsaida dan takarar shugaban kasa daya da zai iya kyara da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Peter Obi, wanda ke takara a inuwar jam'iyyar NDC da Gwamna Seyi Makinde na APM na cikin wadanda ake sa ran za su hada kai gabanin ranar babban zaben 2027.
Madugun adawar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC na cikin wadanda ake fatan za su kulla kawance gabanin zaben.
Sai dai yayin da jam'iyyu suka fara bude fagen yakin neman zabe, an ga Peter Obi ya halarci taron kaddamar da ofishin yakin neman zaben gwamna Makinde.

Kara karanta wannan
Maimakon dawo da tallafin mai, gwamna ya kawo hanyar karya farashin fetur a Najeriya
Da yake jawabi a wurin taron, Peter Obi ya ce bai kamata neman shugabancin Najeriya ya kasance bisa son rai ko gaba tsakanin 'yan siyasa ba, yana mai jira ga hadin kai don kawo ci gaban kasa.
Tsohon gwamnan ya bukaci 'yan siyasa su daina mayar da hankali kan sabani tsakaninsu da kuma gaba. Ya ce ya kamata su karkata karfinsu wajen magance matsalolin da 'yan Najeriya ke fuskanta.
Asali: Legit.ng