Babbar Matsalar da ke Neman Ɓata Shirin Hadakar Tsayar da Ɗan Takarar 1 a 2027

Babbar Matsalar da ke Neman Ɓata Shirin Hadakar Tsayar da Ɗan Takarar 1 a 2027

  • Jam’iyyun adawa na shirin hada kai wajen tsayar da dan takara daya a 2027, tare da yi masa alkawarin wa’adin da zai yi
  • Masana sun ce alkawarin wa’adin daya ba zai iya shafe damar neman wa’adi na biyu da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bayar ba
  • Masu sharhi sun bukaci jam’iyyun adawa su gabatar da cikakken shiri, kundin yarjejeniya da hanyoyin tabbatar da alkawarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Yunkurin jam’iyyun adawa na gabatar da dan takara daya a zaben 2027 ya haifar da muhawara kan yiwuwar aiwatar da shirin.

Jam’iyyun sun tsara cewa wanda zai lashe zaben zai yi mulki na shekaru hudu kacal, ba tare da neman wa’adi na biyu ba.

Shirin hadakar yan adawa na neman samun matsala
Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Peter Obi. Hoto: Atiku Abubakar, Bayo Onanuga, Mr Peter Obi.
Source: Twitter

Matsalar da za a iya samu a shirin

Sai dai masana sun nuna shakku kan yiwuwar tabbatar da irin wannan alkawari, musamman saboda tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Shirin cire Tinubu a mulki: Jam'iyyar PDP ta fadi matsayarta kan hadaka a 2027

A halin yanzu, kundin tsarin mulkin kasar bai hana shugaban kasa neman wa’adi na biyu ba bayan ya kammala wa’adinsa na farko.

Babban abin da shirin ke kokarin cimmawa shi ne daidaita burin ’yan takarar adawa da kuma samar da hadin kai.

Hakan zai baiwa jam’iyyun adawa damar kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a babban zaben 2027.

Masu goyon bayan shirin na ganin cewa hakan zai samar wa Najeriya wata sahihiyar madadin gwamnati.

Tinubu na shan matsin lamba kan zaben 2027
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da ke neman wa'adi na 2. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Ganawar kungiyar G-100 kan hadaka

A ranar Litinin da ta gabata, jam’iyyun adawa da masu ruwa da tsaki sun taru a Abuja karkashin kungiyar G-100.

Taron ya gabatar da tsarin gwamnatin kwarewar kasa wanda zai kasance karkashin wa’adin sauyi na shekaru hudu.

An kuma samar da kungiyoyi biyar da za su tsara yarjejeniyar wa’adin daya da kuma hanyar samar da dan takara daya.

Tsarin G-100 ya kuma kunshi shirin sake fasalin Najeriya cikin shekaru hudu, wanda aka bayyana a matsayin National Reset Programme.

Kara karanta wannan

2027: 'Yan adawa sun kafa kwamitin fitar da tsarin kayar da APC a kwana 30

Wannan shiri ya zo ne a lokacin da siyasar neman wa’adi na biyu ta zama muhimmin bangare na zabukan Najeriya.

Masu goyon bayan tsarin sun ce wa’adin daya zai baiwa shugaban damar aiwatar da sauye-sauye ba tare da damuwa da neman zabe ba.

Amma masu suka sun ce alkawarin siyasa ne kawai idan ba a tabbatar da shi ta hanyar gyaran kundin tsarin mulki ba.

Masana shari’a da siyasa, kungiyoyin fararen hula da kungiyoyin yankuna sun nuna shakku kan yiwuwar shirin.

Idan ba a samar da tsarin da zai sasanta bukatun ’yan takara daban-daban ba, kawancen na iya rushewa.

Zaben 2027: Kungiya na shirin kan yan adawa

A baya, an ji cewa kungiyar G-100 za ta gudanar da taron hadin kan jam’iyyun adawa a Abuja ranar 18 ga watan Agusta, 2026, gabanin zaben 2027.

Kungiyar ta gana da shugabannin jam’iyyun adawa shida domin tattauna yadda za a samar da hadin kai.

Yan G-100 sun ce hadin kan adawa zai bukaci sadaukarwa da sassauci daga shugabannin jam’iyyun na adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.