Shugaban APC Ya Yi Kaca Kaca da Yunkurin Yan Adawa na Tsaida Dan Takarar Shugaban Kasa 1 a 2027

Shugaban APC Ya Yi Kaca Kaca da Yunkurin Yan Adawa na Tsaida Dan Takarar Shugaban Kasa 1 a 2027

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta yi watsi da taron jam'iyyun adawa, tana mai cewa yunƙurinsu ba zai kai ga nasara ba
  • Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam'iyyun sun makara wajen fara shirye-shiryen tunkarar zaben 2027
  • Ministan sufurin jiragen sama da harkokin sararin samaniya, Festus Keyamo ya bayyana yunƙurin hadakar a matsayin tafiyar da ba za ta je ko'ina ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta yi watsi da sabon taron da manyan jam'iyyun adawa suka gudanar a Najeriya, tana mai cewa yunƙurin haɗin gwiwar nasu ya riga ya gaza tun kafin fara aiki.

Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce taron ya nuna fargabar da ke tattare da 'yan adawa kan abin da yake ganin zai zama mummunar shan kashi a babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

An kalubalanci Tinubu ya yi tafiya a mota idan ya gamsu da tsaro a Najeriya

Nentawe.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda a ofis da ke Abuja Hoto: @Nentawe1
Source: Twitter

Leadership ta ruwaito cewanYilwatda ya bayyana taron da kungiyar G100 ta shirya domin yan adawa su zabi dan takara daya da zai gwabza da Shugaba Bola Tinubu, a matsayin wani abu da "ya mutu tun kafin ya fara."

APC ta soki shirin jam'iyyun adawa

Da yake magana ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, Abimbola Tooki, shugaban APC ya ce bai dace jam'iyyun adawa su fara neman hanyar samun nasara a yanzu ba.

A cewarsa, idan har ba su iya tsara kansu cikin shekaru hudu ba, zai zama abu mai wuya su yi gaggawar neman nasara cikin kankanin lokaci.

Ya ce:

"Dukkansu suna kokarin kare muradunsu na kashin kansu. Tambayar ita ce, me suke yi a cikin shekaru hudu da suka gabata? Yanzu saura watanni hudu a yi zabe, sai kwatsam suka farka daga barci. Haka ake yi?"

Ministan Tinubu ya yi martani

Kara karanta wannan

2027: Jam'iyyar NDC ta su Kwankwaso ta fitar da sunayen yan takarar gwamna a jihohi 12

Shi ma ministan sufurin jiragen sama da harkokin sararin samaniya, Festus Keyamo, SAN, ya bayyana yunƙurin hadakar a matsayin "tafiyar da ba ta zuwa ko'ina."

Keyamo ya ce abin da ya faru a taron ya tabbatar da matsayinsa na farko kan batun.

Ya shaida wa Vanguard cewa:

"Dukkan lamarin yana nuna cewa sun amince da za su sha mummunan kaye a 2027. Mafi alherin abin da za su yi shi ne su janye cikin mutunci tare da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya."
Manyan yan adawa.
Manyan yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun adawa, Peter Obi da Atiki Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Jam'iyyun adawa sun yi taro

Martanin APC ya biyo bayan taron farko da manyan jam'iyyun adawa shida suka gudanar a Abuja a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, 2026.

Jam'iyyun da suka halarci taron sun hada da ADC, APM, NDC, wani bangare na PDP, PRP da SDP.

Matsalar da ke tunkarar yan adawa

Kun ji cewa yunkurin jam’iyyun adawa na gabatar da dan takara daya a zaben 2027 ya haifar da muhawara kan yiwuwar aiwatar da shirin.

Jam’iyyun sun tsara cewa wanda zai lashe zaben zai yi mulki na shekaru hudu kacal, ba tare da neman wa’adi na biyu ba.

Sai dai masana sun nuna shakku kan yiwuwar tabbatar da irin wannan alkawari, musamman saboda tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262