Tinubu Ya Tafka Kura Kurai a Gwamnati, Ana Ganin Za Su Jawo Ya Sha Kaye a Zaben 2027

Tinubu Ya Tafka Kura Kurai a Gwamnati, Ana Ganin Za Su Jawo Ya Sha Kaye a Zaben 2027

  • Lawal Daura ya ce Shugaba Bola Tinubu ba mutum ne da ba za a iya kayar da shi a zaben shugaban kasa na 2027 ba
  • Dan takarar mataimakin shugaban kasa na APM ya ce gwamnatin Tinubu ta yi kura-kurai da dama da suka jawo mata nakasu a zabe
  • Daura ya ce shi da Seyi Makinde suna da manufa guda ta farfado da Najeriya, kuma sun shirya tunkarar kowane kalubale

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na APM, Lawal Daura, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu bai fi karfin a kayar da shi a zaben shugaban kasa na 2027 ba.

Lawal Daura ya ce gwamnatin Tinubu ta tafka kura-kurai da dama, wadanda za su iya kawo karshenta a babban zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2027: Peter Obi ya bayyana gwamna 1 da ya cancanci zama shugaban ƙasar Najeriya

Seyi Makinde.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APM, Seyi Makinde da abokin takararsa, Lawal Daura
Source: Facebook

Daura ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television ranar Litinin.

Hakan ya faru ne sa'o'i bayan jam'iyyar APM, wadda ta tsayar da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin dan takararta na shugaban kasa a 2027, ta kaddamar da ofishin yakin neman zabenta a Abuja.

Daura ya hango kura-kuran Tinubu

Tsohon shugaban hukumar tsaro ta DSS ya bayyana Tinubu a matsayin mutum mai saukin kai. Sai dai ya ce ana iya kayar da shugaban kasar a zaben 2027 saboda kura-kurai masu yawa da gwamnatin sa ta yi.

Da aka tambaye shi ko yana ganin za a iya kayar da Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027, Daura ya ce, "sosai kuwa."

Ya kara da cewa:

"Ana cewa babu wanda ya cika kamala, musamman idan kai dan siyasa ne, kana iya aikata kura-kurai da dama, ko da kuwa ba da gangan ka yi su ba."

Kara karanta wannan

Duk da shirin haɗakar yan adawa, Jigon PDP ya sallama wa Shugaba Tinubu a zaben 2027

Da aka sake tambayarsa ko gwamnatin Tinubu tana aikata kura-kurai, sai ya amsa: "Sosai kuwa."

Matsayar APM kan kura-kuran gwamnati

Da aka tambayi Daura ko jam'iyyarsa ta APM za ta yi anfani da kura-kuran da ya ce gwamnatin Tinubu ke yi, ya ce ba wai suna neman anfani da su ba ne.

A cewarsa:

"Ba wai muna anfani da su ba ne, a maimakon haka muna taimakawa wajen gyara kura-kuran. Amma wasu jami'ai da ba su iya aikinsu ko kuma ba su fahimci abin da muke gani ba, watakila ba za su bari a yi anfani da hakan ba."
Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Makinde ya tabo batun tallafin mai

A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APM, Gwamna Seyi Makinde, ya yi watsi da batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya.

Makinde, wanda shi ne gwamnan jihar Oyo , ya ce kamata ya yi a mayar da hankali wajen nemo hanyoyin da za a rage farashin fetur ga 'yan Najeriya.

Makinde yana mayar da martani ne kan yadda wasu suka fahimci wata takarda da ya wallafa kwanan nan, inda ya bayyana matsayarsa kan tallafin man fetur da kuma tsarinsa mai suna Reset Nigeria Agenda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262