Yayin da Tinubu Ya Ki, Gwamnatin Jamus Ta Saka Tallafin Man Fetur
- Masu abubuwan hawa a Jamus sun fara amfana da rangwamen farashin man fetur da diesel daga ranar Alhamis, 1 ga Okotoban 2026
- Farashin man ya ragu da kusan cent 14 zuwa 15 a kowace lita, yayin da gwamnati ke kokarin rage tasirin tashin farashin makamashi
- Rangwamen ya zo ne yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke kawo cikas ga samar da man fetur tare da kara tsadar makamashi a kasashen Turai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jamus – Masu abubuwan hawa a Jamus sun fara samun rangwamen farashin man fetur da dizil daga ranar Alhamis, yayin da gwamnatin kasar ke kokarin rage musu radadin tashin farashin makamashi sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.
Farashin man fetur ya ragu da kusan cent 14, yayin da diesel ya ragu da cent 15 a kowace lita, a cewar kungiyar masu abubuwan hawa ta Jamus, ADAC.

Source: Getty Images
Farashin man fetur ya ragu a Jamus
ADAC ta shaida wa AFP cewa da misalin karfe 12:15 na rana a ranar Alhamis, masu amfani da man fetur sun biya kasa da cent 14 zuwa 15 idan aka kwatanta da ranar Laraba, gwargwadon irin man da suka saya.
Rahotanni sun ce farashin litar man fetur ya sauka zuwa kusan Euro 2.06, yayin da diesel ya koma kusan Euro 2.20 a kowace lita.
Gwamnatin Jamus ta amince da rangwamen harajin makamashi da ya kai cent 17 kan kowace lita, matakin da zai ci gaba daga farkon watan Oktoba zuwa karshen shekarar 2026.
Dalilin kara tsadar mai
Rikicin Gabas ta Tsakiya ya janyo tashin farashin man fetur a Jamus da sauran kasashe, yayin da yake kawo cikas ga samar da man fetur daga yankin.
Rahoto ya nuna cewa sababbin dokokin da gwamnatin Jamus ta sanya sun bai wa gidajen sayar da man damar kara farashin sau daya kacal a rana, da karfe 12 na rana.
ADAC ta ce duk da gagarumin karin farashin da aka samu da tsakar ranar Alhamis, farashin ya ci gaba da kasancewa kasa da wanda aka samu a daidai wannan lokaci a ranar Laraba.
Sai dai wasu masu abubuwan hawa sun ce rangwamen bai wadatar ba, musamman ganin yadda farashin man yake da tsada.
France 24 ta wallafa cewa wata mazauniyar Frankfurt mai suna Andrea Hoecker, mai shekaru 33, ta ce rangwamen ya yi kadan har yanzu, tana bukatar a kara rage shi.

Source: AFP
Maganar tallafin mai a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ba za ta koma tsarin tallafin man fetur da aka cire a shekarar 2023 ba.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya bayyana hakan ne a Abuja yayin lacca ta musamman da aka shirya domin bikin cika shekaru 66 da samun 'yancin kan Najeriya.
A bayanin da ya yi, Sanata Akume ya ce cire tallafin na daga cikin matakan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta dauka domin daidaita tattalin arzikin Najeriya.
Asali: Legit.ng

