Tsohon Shugaban DSS Ya Yi Maganar yadda Na Kusa Suka Yaudari Buhari
- Lawal Daura yana da ra’ayin cewa wasu mutanen Muhammadu Buhari suka jawo wa gwamnatinsa matsala
- Tsohon shugaban DSS ya ce an dauko mutanen da ba su dace ba, aka ba su mukaman da suka fi karfinsu
- Daura ya zargi na kusa da Buhari da cin amanarsa, ya kuma kore zargin cewa akwai masu juya shugaban kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Lawal Musa Daura wanda ya shugabanci hukumar DSS ta kasa ya tofa albarkacin bakinsa game da gwamnatin Muhammadu Buhari.
Lawal Daura ya yi zargin cewa akwai wasu mutane da suka zagaye marigayi Muhammadu Buhari wadanda su suka ci amanarsa.

Source: UGC
Lawal Daura ya kare gwamnatin Muhammadu Buhari
A wata zantawa da aka yi da shi a tashar Channels TV, Alhaji Lawal Daura ya ba gwamnatin da ta wuce uzuri, ya kuma ba ta kariya.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tafka kura kurai a gwamnati, ana ganin za su jawo ya sha kaye a zaben 2027
‘Dan takaran na mataimakin shugaban kasa ya ce masu cewa ba a taba mummunar gwamnati kamar ta Buhari ba suka sake yin nazari.
Ya ce ya kamata su duba gwamnatocin da aka yi daga 1995 zuwa 2023 kafin su fadi haka.
Dangatakar tsohon shugaban DSS da Buhari
A matsayinsa na shugaban DSS, Daura ya bayyana cewa aikinsa ya sa yana da kusanci sosai da Buhari lokacin da yake fadar Aso Rock.
Daura ya ce ya tsaya wa marigayin kuma ya kare gwamnatinsa a matsayin shugaban DSS, lamarin da ya ce ya canza da ya bar kujerar.
“Wannan zai nuna maka na tsaya masa kuma na kare gwamnatinsa. Komai ya nemi ya canza bayan 2018 na bar ofis.”
- Lawal Daura
Su wane ne suka ci amanar Buhari?
Game da batun wadanda suka zagaye Buhari, tsohon jami’in tsaron ya ce ya san wasunsu da kuma abubuwan da suka rika yi lokacin.
Alhaji Daura yana da cikakken bayanin wasu abubuwan da suka yi sai dai ya karyata ikirarin da ake yi na cewa akwai wasu miyagu a fadar.
Sai dai bai zarge su da yaudarar Buhari ba, amma yana ganin sun ci amanar yardar da ya ya yi da su.
Ya ce gwamnatin Mai girma Buhari ta yi ta shan wahala na shekarun ne saboda an dauko mutanen da ba su cancanta ba, an ba su mukamai.
Sabon shiga siyasar ya ce bai kamata yardar mutum ko amannar shi da marigayin kawai ta zama abin la’akari da shi wajen ba shi kujera ba.
Akwai masu juya gwamnatin Buhari ta bayen-fage?
The Cable ta rahoto shi yana cewa bai cikin wadanda ake ta zargin su ne asalin masu juya madafun iko a boye da Buhari yake kan karaga.
Lawal Daura ya ce:
“A’a, babu wasu miyagu.
"Idan ma akwai su, babban jami’in leken asirin kasar ba zai taba zama cikin miyagun ba saboda aikin da yake gaba na ba ya sa a kullum ina kusa da shugaban kasar."

Source: Getty Images
Minista ta tabo zancen magajin Tinubu
Ana da labari Karamar Ministar harkokin Abuja ta ga Bola Tinubu ya zarce, ta yi zancen wanda zai gaji kujerar shugaban kasa a Mayun 2031.
Mariya Mahmud Bunkure ta ce Aso Rock ba za ta yi sabon ango a shekara mai zuwa, ta yi maganar ne lokacin gana wa da 'yan kungiyar City Boy.
Ministar Abuja tana sa ran Shugaba Bola Tinubu yana Aso Rock har zuwa shekara ta 2031, sannan ya mika wa dan jam’iyyar APC mulkin kasa.
Asali: Legit.ng

