Tashin Hankali: Ministan Tsaron Isra'ila Ya Dura Masallaci na 3 Mafi Daraja a wurin Musulmai

Tashin Hankali: Ministan Tsaron Isra'ila Ya Dura Masallaci na 3 Mafi Daraja a wurin Musulmai

  • Ofishin Ministan Tsaron Cikin Gida na Isra’ila, Itamar Ben-Gvir, ya fitar da wani bidiyo da ke nuna shi yana shiga harabar Masallacin Al-Aqsa
  • An ga dan siyasar masu tsattsauran ra’ayi ne karkashin rakiyar ‘yan sandan Isra’ila yayin bikin Sukkot na Yahudawa, inda aka ce ya gudanar da wasu ibadun addini
  • Ma’aikatar kula da harkokin addini ta Falasdinawa ta ce irin wadannan ayyuka na neman ruruta yakin addini a yankin baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Isra'ila - Ministan Tsaron Cikin Gida na Isra’ila, Itamar Ben-Gvir, ya fitar da wani bidiyo da ke nuna shi yana shiga harabar Masallacin Al-Aqsa, masallaci mai daraja ta uku a wurin musulmai.

Bidiyon ya nuna dan siyasar masu tsattsauran ra’ayi karkashin kariyar ‘yan sandan Isra’ila yayin bikin Sukkot na Yahudawa. Rahotanni sun ce ya gudanar da wasu ibadun addini a wurin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu za ta ci bashin biliyoyin daloli a bankin duniya

Itamar Ben-Gvir
Ministan tsaron cikin gida na Isra'ila, Itamar Ben-Gvir kewaye da yan sanda yana daga hannu Hoto: Erik Marmor/Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa karkashin yarjejeniyar “status quo” da Isra’ila ta amince da ita tun 1967, gwamnatin Isra’ila ta bar hukumar Waqf da Jordan ta naɗa, ta ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum a msallacin.

Haka zalika, yarjejeniyar ta kuma tanadi cewa Musulmi ne kadai za su yi ibada a wannan wurin.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262