Muhimman batutuwa 5 da ya kamata ku sani game da Lawal Daura, korarran shugaban hukumar DSS
Biyo bayan rahotannin da muka samu da da suka tabbatar mana da cewa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tsige shugaban hukumar tsaro ta sirri, wato DSS, Malam Lawal Daura daga mukaminsa a dazun nan, mun shiga bincike domin zakulo maku wasu bayanai game da shi.
Wani labarin kuma da muka samu yace an tsige shi ne saboda farmakin da jami’an hukumar suka kai majalisar dokokin Najeriya da safiyar ranar Talata 7 ga watan Agusta.
KU KARANTA: Dalilin da yasa na tsige Lawal Daura - Osinbajo
Legit.ng ta samu haka zalika cewa hadimin shugaban kasa Buhari akan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya tabbatar da fatattakar Lawal Daura daga aiki. Bugu da kari, Farfesa Osinbajo ya umarci Lawal Daura ya mika ragamar tafiyar da hukumar ga jami’I mafi girma a hukumar, har sai baba ta ji.
Ga dai wasu Muhimman batutuwa 5 da ya kamata ku sani game da shi:
1. An haife shi ne a ranar 5 ga watan Agusta, 1953.
2. Ya fito ne daga karamar hukumar Daura, jihar Katsina.
3. Yayi karatun sa na jami'a ne a jami'ar ABU, Zaria.
4. Ya fara aikin jami'in tsaron farin kaya a shekarar 1982.
5. Shugaba Buhari ya nada shi shugaban hukumar tsaron farin kaya ta DSS a ranar 2 ga watan Yuli, 2015.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng